Sai da Umara Zulum da Ben Ayade su ka kai Farfesa kafin su zama Gwamna

Sai da Umara Zulum da Ben Ayade su ka kai Farfesa kafin su zama Gwamna

Legit.ng Hausa ta kawo maku jerin zakakuran gwamnonin da su ka yi fice wajen karatun boko a Najeriya. Wadannan gwamnoni sun hada ilmin zamani da aikin siyasa.

Wasu gwamnonin jihohi ne wadannan:

1. Ben Ayade

Gwamna Ayade ya yi Digiri na daya har zuwa na uku a jami’ar Ibadan a ilmin kananan halittu. Bayan haka gwamnan ya yi Digiri a bangaren shari’a, kuma yanzu ya koma ya yi Digirgrir.

Ayade wanda Farfesa ne ya kuma yi Digirin MBA a kan fannin kasuwanci a wata jami’a a Delta.

2. Babagana Umara Zulum

Gwamnan jihar Borno watau Babagana Zulum shi ma Farfesa ne domin ya yi Digiri na farko zuw ana uku a bangaren fasahar noma da ruwa. Gwamna Zulum Masani ne a harkar noman rani.

3. Kayode Fayemi

Gwamna na uku a jerin shi ne Kayode Fayemi na jihar Ekiti wanda ya yi Digirin farko a ilmin tarihi da siyasa a Legas. Daga baya ya samu Digirgir a harkar huldar kasashen waje a OAU.

Daga baya Fayemi ya zama Daktan boko inda ya yi Digirin PhD a wata jami’a da ke Landan.

Sai da Umara Zulum da Ben Ayade su ka kai Farfesa kafin su zama Gwamna

Farfesa Ben Ayade ya na Digiri 5 amma bai hakura da boko ba
Source: UGC

KU KARANTA: Yadda mutanen Ibo za su samu mulkin Najeriya - Sama Isa

4. Abdullahi Umar Ganduje

Mai girma gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya halarci Jami’ar ABU ta Zariya sau biyu, ya kuma samu Digirin farko a harkar koyarwa da na biyu a bangaren sha’anin jagoranci, a shekarun baya.

Bayan haka Ganduje ya yi Digirgir a Jami’ar Bayero, a 1993 kuma ya gama PhD a jami’ar Ibadan.

5. Nasir El-Rufai

Na karshe a jerin na mu shi ne Malam Nasir El-Rufai wanda shi har yau ba a manta da tarihinsa a jami’ar Ahmadu Bello ba. Nasir El-Rufai ya yi wani Digirin a ilmin shari’a a Landan a 2009.

Bayan haka Gwamnan ya yi Digirin MPA a Amurka. Yanzu haka, ya sake komawa PhD a waje.

Bayan wadannan gwamnoni akwai kuma irinsu Alhaji Abdullahi Sule, Cif Willie Obiano da Mista Adegboyega Oyetola wanda duk sun yi Digiri da Digirgir a bangarorin ilmin boko iri-iri.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel