Kogi: Mutum fiye da 20 su ka mutu a ta’adin da aka yi a Kauyen Tawari

Kogi: Mutum fiye da 20 su ka mutu a ta’adin da aka yi a Kauyen Tawari

Mun ji cewa mummunan hari da aka kai da daren Ranar Juma’a a, 3 ga Watan Junairu, 2019, a jihar Kogi ya yi sanadiyyar kashe mutane fiye da 20.

Kamar yadda labari ya zo, wani Limami ya na cikin wadanda su ka mutu a harin da aka kai wa Kauyen Tawari da kimanin karfe 1:00 na tsakar daren.

Jaridar Daily Trust ta ce wasu Miyagun Makiyaya ne wanda sun kai akalla mutum 100 su ka shiga wannan Kauye su ka rika harba bindiga ko ta ina.

Yanzu an tabbatar da cewa shugaban jam’iyyar APC na Mazabar Tawari, Ibrahim Simbabi ya na cikin wadanda su ka rasa ran su a wannan harin.

Haka zalika babban Limamin wannan Kauye, Malam Zakari Salihu ya na cikin wadanda su ka bakunci barzahu a sakamakon harin Makiyayan.

KU KARANTA: Kungiyoyin Kabilun Najeriya sun ba Buhari shawarwari

Kogi: Mutum fiye da 20 su ka mutu a ta’adin da aka yi a Kauyen Tawari
Harin da aka kai Ranar Juma'a a Kogi ya kashe mutum 23
Asali: Facebook

Rahotanni sun ce wadannan Miyagun mutane da su ka dura Tawari cikin dare, sun ruguza tsohon dakin shan maganin da Turawa su ka gina a Kauyen.

Ba a nan kurum muguwar wannan barna ta tsaya ba, an kuma kona motar Mai unguwar Yankin watau Mai martaba Aguman Tawari, Alhaji Idris Tawari.

Bayan wannan asara da Idris Tawari ya fuskanta na kona masa abin hawa, an kuma yi masa tabargaza iri-iri, aka lalata kayan arzikin da ya mallaka.

Kantoman karamar hukumar, Musa Tanko Mohammed, ya ce an kashe mutane 19. Amma mutane sun kirga gawar mutane har 23 yayin da wasu ke asibiti.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel