Burina na yi ayyukan da Allah zai kalle ni da idon rahama a gobe kiyama – Obasanjo

Burina na yi ayyukan da Allah zai kalle ni da idon rahama a gobe kiyama – Obasanjo

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana sadaukar da dukkanin nasarorin daya samu a rayuwarsa a lokacin da ya yi shugabanci a karkashin tsarin mulkin Soja da na mulkin dimukradiyya ga Allah Ubangiji.

Obasanjo ya bayyana haka ne yayin wani taron addua da godiya da kungiyar kiristocin Najeriya reshen jahar Ogun, ta shirya masa a cocinsa dake garin Abekuta, inda yace Allah Ya yi masa falala da dama, don haka zai cigaba da yin duk abin da zai sa Allah Ya yi masa rahama gobe kiyama.

KU KARANTA: Siyasa rigar yanci: Dan majalisa ya baiwa mutane 220 mukamin masu bashi shawara

“Allah Ya yi min falala da dama, don haka nake son In yi duk abin da zai sa Allah Ya yi min rahama, b azan iya yi ma Allah karya ba. Wadanda suka san kauyenmu Ibogun-Olaogun sun san karamin wuri ne, amma Allah Ya daga ni na kai wannan matsayi a rayuwa na cimma nasarori da dama.

“Na fada na nanata, duk nasarar da na samu ba ta yiwuwa sai tare da wasu mutane da suka taimaka min, wasu na raye, wasu kuma sun mutu, don haka da ba don su ba da ban samu wata nasara ba.” Inji shi.

Shi ma a nasa jawabin, gwamnan jahar Ogun, Dapo Abiodun ya bayyana nasarar daya samu a kotun kolin Najeriya ga rahamar Ubangiji, don haka ya yi alkawarin zai yi mulki na adalci da gaskiya da rikon amana.

Daga karshe Gwamna Dapo ya yi kira ga jama’an jahar dasu bashi goyon baya don samar da cigaba mai daurewa a jahar. Sa’annan ya bayyana Obasanjo a matsayi shahararren mutum abin alfahari ga jahar Ogun, kuma jakadan duniya dan kasa nagari.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai tsohon gwamnan jahar Ogun, Gbenga Daniel, tsohon gwamnan jahar Ekiti, Segun Oni, shugaban bankin cigaban Afirka, Akinwumi Adesina, hamshakin dan kasuwa Cif Kessignton Adebutu da sauransu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng