Masallatai 5 mafi kyau a Najeriya
Addinin Musulunci shine addini mafi shahara da mabiya a Najeriya da nahiyar Afirka. Kana addinin na da gine-gine na goge raini wanda ko mabiya wasu addinai na sha’awa.
Jaridar Legit.ng ta kawo muku jerin masallatai mafi kyawu a fadin Najeriya.
1.Masallacin Bashir Uthman Tofa
Masallacin Bashir Tofa na daga cikin manyan masallatai a Najeriya. Masallacin na zaune a Gandu Albasa, jihar Kano.
2. Masallacin jihar Kano
Muhammad Zaki ya mayar da wannan babban Masallaci sabon wuri ne a shekarar 1582 kuma sarkin Kano, Abdullahi dan Dabo ya sake ginawa tsakanin shekaran 1855 da 1883. Bayan lalacewanshi a shekarun 1950, gwamnatin Birtaniya ta dauki nauyin sake ginashi.
3. Masallacin birnin tarayya, Abuja
An gina babban masallacin birnin tarayya a shekaran 1942 a tsakiyan birnin tarayya. Wannan masallaci har ila yau ya nada kyanshi tamkar yau aka gina.
4. Masallacin Ilori
A baya-bayan nan, an gina masallaci a garin Ilori wanda ke iya daukan masallata 20,000 a lokaci gda. An gina masallacin ne siffan masallacin manzon Allah ﷺ da ke Madina.
5. Masallacin jihar Legas
An gina masallacin jihar Legas ne a shekaran 1841. Kuma har ila yau yana nan bayan shekaru 160
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng