Kotu ta amince EFCC ta cigaba da tsare tsohon ministan shari'a na tsawon kwanaki 14

Kotu ta amince EFCC ta cigaba da tsare tsohon ministan shari'a na tsawon kwanaki 14

A ranar Alhamis ne wata kotun tarayya a karkashin mai shari'a, Jastis A. O Musa, dake Abuja ta bawa hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) izinin cigaba da tsare tsohon ministan shari'a, Mohammed Bello Adoke, na tsawon kwanaki 14.

Hukumar EFCC ce ta nemi kotun ta bata izinin cigaba da tsare Adoke har zuwa lokacin da zata kammala shiri domin gurfanar da shi a gaban kotu.

Da yake yanke hukunci a kan bukatar da EFCC ta mika a gaban kotunsa, Jastis Musa ya bayyana cewa, "bukatar neman a tsare wanda ake zargi na tsawon kwanaki 14 domin a gurfanar da shi ya zama wajibi, a saboda haka wannan kotu ta amince da bukatar masu kara."

A ranar 19 ga watan Disamba na shekarar 2019 ne hukumar EFCC ta cafke Adoke bayan dawowarsa daga kasar Dubai dake hadaddiyar daular Larabawa.

A wani labarin mai nasaba da wannan, Legit.ng ta rawaito cewa hukumar EFCC ta samu yardar kotu na tsare Sanata Shehu Sani har tsawon kwanaki 14 domin bayar da damar bincike kan zarginsa da hannu a badakalar wasu kudade.

Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kamfanin motar ASD, Alhaji Sani Dauda, ya yi watsi da ikirarin Shehu Sani, inda yace lallai yana kan bakarsa kan korafin da ake kan sanatan.

Kotu ta amince EFCC ta cigaba da tsare tsohon ministan shari'a na tsawon kwanaki 14
Adoke
Asali: Facebook

Korafin ya kuma yi zargin cewa Shehu Sani ya ajiye sunan shugaban alkalan Najeriya, inda ya bukaci ya biya naira miliyan 4 wanda shi shugaban alkalan zai raba ma alkalai 4 da za su tabbatar da ganin cewar karar da wani Abubakar ya shigar kan shugaban na ASD bai cimma nasara ba.

Korafin ya kuma yi zargin cewa sanatan ya bukaci naira miliyan 1 ga jami’an EFCC. Ya kara da cewa ya biya naira miliyan 5 a dala ga alkalan hudu da jami’an EFCC ta hannun Shehu Sani.

DUBA WANNAN: Kaduna: Gobara ta kone mai jego, jariri da mutane uku a Rigasa

Ya kuma yi ikirarin cewa sanatan ya dawo a ranar 29 ga watan Nuwamba, 2019, cewa mai kara kan shari'arsa ba zai iya yin komai ba amma ya yi magana da Magu ya ce ya kawo $20,000 don magance lamarin. Ya yi zargin cewa ya shiga juyayi ganin cewa Magu baya rashawa.

Amma Sanatan ya yi zargin cewa Magu abokinsa ne sannan cewa zai karbi cin hanci. Mai karar ya ci gaba da cewa ya ba Shehu Sani $10,000 a ranar 29 ga watan Nuwamba, 2019.

Ya kuma yi zargin cewa tun aga lokacin Shehu Sani ya daina daukar wayarsa sannan ya yi buris da sakonninsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel