Yibo Koko ya zama DG a karkashin Gwamnatin Nyesom Wike

Yibo Koko ya zama DG a karkashin Gwamnatin Nyesom Wike

Mai girma gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi nadin wani sabon mukami kamar yadda mu ka samu labari dazu.

Nyesom Wike ya nada Yibo Koko a matsayin Darekta Janar na hukumar da ke kula da harkar shakatawa ta jihar Ribas.

Mista Yibo Koko fitaccen ‘Dan wasan barkwanci ne wanda ya kware wajen ba Bayin Allah dariya domin ya samu na abinci.

Haka zalika Koko ya kan shirya wasanni kuma ya rubuta a gidan talabijin, ya yi kaurin-suna a harkar wasan kwaikwayo.

Bayan irin baiwar da Yibo Koko ya mora wajen wasan kwaikwayo da barkwanci, ya yi karatun boko na zamani mai zurfi.

KU KARANTA: An ba Buhari shawara ya nada sababbin hafsun Soji a Najeriya

Yibo Koko ya zama DG a karkashin Gwamnatin Nyesom Wike

Koko zai rika kula da hukumar harkar shakatawa a Ribas.
Source: Depositphotos

Binciken da Legit.ng ta yi ya nuna cewa kafin yanzu sabon Darektan ya yi aiki a shararren shirin nan na ‘Nigeria’s Got Talent’

Koko ya na cikin manyan Alkalan da ke zaben ‘Yan Baiwa a wannan shiri da a kan yi a gidajen talabijin a fadin Najeriya.

Sakataren gwamnatin Ribas, Tammy Danagogo, shi ne ya bada sanarwar wannan nadi da aka yi a Ranar 2 ga Watan Junairu.

A Ranar Alhamis, Dr. Tammy Danagogo ya shaida cewa Yibo Koko zai fara aiki a ofishinsa ne ba tare da wani bata lokaci ba.

Idan ku na bibiyar sha’anin nishadi, za ku san cewa Yibi Koko ne ya kirkiro rawar zamanin nan da ake kira Seki a Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Online view pixel