A karshe: Wanda ya kitsa fashin bankin Abuja ya shiga hannu

A karshe: Wanda ya kitsa fashin bankin Abuja ya shiga hannu

Rundunar yan sandan birnin tarayya ta ce ta kama wani Ernest Ewim, wanda ake zargi da shirya fashin bankin da aka dakile, wanda ya afku a yankin Mpape na Abuja a ranar 28 ga watan Disamba 2019.

Kakakin rundunar, DSP Anjuguri Manzah ya tabbatar da lamarin a wani jawabi da ya fitar.

A cewar jawabin, tawagar jami'an yan sanda ne suka kama mai laifin wanda ya taka muhimmiyar rawar gani a fashin bakin da aka dakile a mabuyarsa ta Katampe 1 a yammacin ranar Laraba, 1 ga watan Janairu.

"A wannan kamun, a yanzu gaba daya an damke jimlar mutane biyar da ke da nasaba da yunkurin fashin banki da aka dakile: Ernest Ewim dan shekara 29, Larry Ehizo dan shekara 30, Princewill Obinna dan shekara 24, Timothy Joe dan shekara 21, da kuma Elijah David dan shekara," cewar jawabin.

KU KARANTA KUMA: Da dumi dumi: Yan bindiga sun kai ma jirgin Kaduna – Abuja hari

Jawabin ya kara da cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarin da take yi na kare lafiya da dukiyoyin mazauna birnin tarayyar. Za kuma a gurfanar da wadanda ake zargi a kotu idan an kammala bincike.

A baya mun ji cewa a ranar 28 ga Watan Disamban 2019, wasu Miyagun mutane su ka nemi su yi fashi a wani bankin First Bank da ke Garin Abuja.

Wadannan ‘Yan fashi sun nemi su yi sata a banki ne da tsakar safe yayin da ido-ke-ganin-ido kuma a Ranar da kaf bankuna ke hutu da fitowa aiki.

A karshe jami’an tsaron da ke dankare a wannan yanki na Mpape inda ake da Barikin Sojojin kasa sun yi ram da wadannan Barayi masu karfin hali.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel