2023: Ɗankwambo ya aike wa 'yan PDP saƙo

2023: Ɗankwambo ya aike wa 'yan PDP saƙo

Tsohon gwamnan jihar Gombe, Alhaji Ibrahim Dankwambo, ya yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar PDP na jihar da su kasance tsintsiya madaurinki daya. Dankwambo yayi wannan kiran ne yayin da yake jawabi a wani taron jam’iyyar a Gombe da aka yi a ranar Litinin.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin tsohon mataimakinsa Charles Iliya, ya ce duk aiyukan cigaban da aka aiwatar a jihar anyi su ne karkashin mulkin PDP. Ya kara da tabbatar da cewa zasu koma mulki nan ba da dadewa ba.

A jawabinsa, shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Nuhu Poloma, ya ce jam’iyyar ta sha kasa ne a zaben 2019 sakamakon sakankancewa. Ya kara da cewa jam’iyyar na da karfi har yanzu a jihar duk da kayen da ta sha.

DUBA WANNAN: Bani da wata matsala da Ganduje - Abdulmumin Jibril

Ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar da su bai wa wadanda suke zaune a jam’iyyar ko bayan da suka sha kaye, tikitin takara a zabe mai zuwa. Kada su saurari wadanda suka bar jam’iyyar saboda halin da suka shiga.

A yayin jawabin shugaban jam’iyyar PDP din na jihar Bauchi, Alhaji Hamza Akunya, ya ce jam’iyyar ta fadi a jihar Gombe ne ba saboda rashin mulki mai kyau ba, sai don saboda aiyukan zagon kasa da wasu ‘yan jam’iyyar suka dinga yi a lokacin.

Ya tabbatar da cewa, wadanda suka bar jam’iyyar zasu dawo nan ba da dadewa ba.

“Shawara ta gareku shine ku zabi wadanda suka cancanta a 2023, kuma wadanda zasu iya kayar da ‘yan takarar sauran jam'iyyun,” yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164