Matasan Yarbawa sun bayyana matsayarsu a kan cigaban mulkin kasa a yankin Arewa

Matasan Yarbawa sun bayyana matsayarsu a kan cigaban mulkin kasa a yankin Arewa

Wata babbar majalisar matasan Yarbawa a ranar Talata ta ce a cikin lumana da zaman lafiya zata soki yunkurin yankin Arewacin kasar nan na cigaba da rike shugabancin Najeriya a 2023.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kammala wa'adin mulkinsa ne nan da shekaru uku, kuma ana ta cece-kuce a kan wanne yankin kasar nan ne zai fitar da shugaban kasa.

Agbarijo Egbe Odo Yoruba tace, ta lura tare da natsewa da komai dake tashe a dangane da zaben 2023.

Majalisar tace, ta gano cewa wasu dattawa a arewa na ta shirin cigaba da rike wannan kujerar, wanda hakan ya ci karo da yarjejeniyar da aka yi a kan kujerar mulkin kasar nan.

Shugaban kungiyar, Kwamared Awa Bamji ya musanta cewa wannan lokacin na yarbawa ne kuma yana kira ga magoya bayan duk wani dan Arewa dake neman kujerar ya janye don neman zaman lafiya.

Bamji ya sanar da hakan ne a bidiyon tattaunawar da yayi da Yerima Shettima, shugaban matasan Arewa, wanda ya yawaita a kafafen sada zumuntar zamani.

Ya ce, Yerima "yana da burin ganin cewa yankin Arewa ya cigaba da shugabanci tun daga 1999 har zuwa 2023..."

DUBA WANNAN: Bani da wata matsala da Ganduje - Abdulmumin Jibril

"Muna ganin cewa, wannan bukatar ta biyo bayan wannan kiran da shugaban dattijan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi yayi, na cewa zasu goyi bayan duk wata jam'iyya ne da ta tsayar da dan Arewa takara a 2023." ya ce.

Wani dattijon Arewa mai suna Junaid Muhammed, ya ce "Arewa sun fi yawa, a don haka koda nan da shekaru 100 ne, su ya kamata su cigaba da mulkin Najeriya."

Kamar yadda shugaban kungiyar matasan Yarbawan ya ce, ya kamata Arewa ta mika shugabanci zuwa wani yankin don ta dade tana mulkar kasar nan.

Bamji ya ce: "Idan zamu kirga yawan shekarun da Arewa tayi tana mulki, zamu gane ta fi Kudu tun daga 1960 har zuwa yau. Rashin daidaituwar tun daga zamanin mulkin soji ne; abinda damokaradiyya ta zo ta gyara. Hakan kuwa zai yuwu ne idan aka mutunta yarjejeniyar shekaru takwas-takwas."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel