Gwamnatin Tarayya ta binciko cuwa-cuwar N27m a Ma’aikatar tsaro

Gwamnatin Tarayya ta binciko cuwa-cuwar N27m a Ma’aikatar tsaro

Gwamnatin tarayya a binciken kudin da ta ke yi duk shekara ta gano cewa akwai alamar tambaya a ma’aikatar tsaron Najeriya.

Rahotanni sun ce binciken da aka gudanar a baya, ya nuna cewa an aikata ba daidai a kan harkar kudi a ma’aikatar na wasu miliyoyi.

Jimillar Naira miliyan 27 ne ake kyautata zaton an karkatar a shekarar 2016 a ma’aikatar kamar yadda mu ka samu labari yau Alhamis.

An fitar da wannan rahoto ne a Ranar Alhamis, 2 ga Watan Junairun 2020, shekaru kusan hudu da zargin aikata wadannan laifuffuka.

Wani babban kwamiti da aka kafa domin gudanar da bukukuwan Ranar tunawa da sojoji ya yi haka-da-haka da Naira miliyan 20.

KU KARANTA: Dakarun Najeriya sun yi wa 'Yan ta'adda luguden wuta

Gwamnatin Tarayya ta binciko cuwa-cuwar N27m a Ma’aikatar tsaro
Janar Mansur Dan Ali ne Minista na lokacin da ake bincike
Asali: Depositphotos

A duk shekara, a Ranar 15 ga Watan Junairu, a kan shirya biki da nufin tunawa da Sojin Najeriya da su ka kwanta dama wajen yaki.

Wannan bincike da gwamnatin tarayya ta yi, ya nuna cewa an kuma yi barna wajen wasu kudi da aka ware na tafiyar Ministan tsaro.

Ministan tsaro na lokacin (Birgediya Janar Mansur Dan-Ali mai ritaya) ya batar da miliyan lokacin da ya halarci wani taro a waje.

An shirya wannan taro na kasashen Duniya da aka yi a kan sha’anin makami mai linzamni ne a Amurka a Ranar 28 ga Watan Maris, 2016.

Ofishin babban Mai binciken kudi a gwamnati ne ya gudanar da wannan aiki kwanaki. Tsohon Ministan bai ce komai ba kawo yanzu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel