Zan rika fitowa ne a fina-finai ne da za su rika fadakar da Jama'a – Dino Melaye

Zan rika fitowa ne a fina-finai ne da za su rika fadakar da Jama'a – Dino Melaye

Sanata Dino Melaye wanda ya wakilci Mazabar Kogi ta Yamma majalisar dattawa, ya yi magana a game da harkar wasan kwaikwayo da ya kan yi.

Gawurtaccen ‘Dan siyasar ya zabi ya bada irin ta sa gudumuwar wajen inganta rayuwar zamantakewar al’umma inda ya fito a wani shirin fim.

Dino Melaye, da ya ke jawabi a Garin Abuja kwanan nan, wajen shirin wasan kwaikwayon da ya fito, ya bayyana cewa kowa ya na da rawar da zai taka.

A cewarsa, fim din ya fito ya ba shi damar fadawa Duniya irin gwagwarmayar da ya shiga a siyasa, da nufin kawo gyara a tsarin shugabanci da mulki.

Tsohon ‘Dan majalisar tarayyar ya ce ya na sa ran sha’anin nishadi saboda muhimmancinsa zai kerewa man fetur wajen kawowa Najeriya tarin arziki.

KU KARANTA:

Zan rika fitowa ne a fina-finai ne da za su rika fadakar da Jama'a – Dino Melaye
Tun ina NYSC na ke shiga wasan kwaikwayo inji Dino Melaye
Asali: Depositphotos

A dalilin haka ne Melaye ya nemi a maida hankali wajen harkar fim. “Karfin tattalin arzikin fina-finai a Amurka ya zarce kasafin kudin Najeriya.”

“Na kawo abin da na sani a harkar siyasa cikin fim ne domin canza al’umma, kuma kowa ya shiga ciki.” Dino ya ce ya kware a harkar wasan kwaiwkwayo.

"Sakon da ke son isarwa shi ne dole a samu shugabannin da su ka san nauyin da ke kansu, Mabiya kuma su rika bibiyar abubuwan da ke faruwa."

Melaye ya ce dole kowa ya tashi tsaye ko kuma kasar ta ruguje, ya kuma bukaci gwamnati ta kawo dokoki da tsare-tsaren da za su taimakawa fim.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng