Ka sanya dokar ta-baci a kan tsaro - Matasan arewa ga Buhari

Ka sanya dokar ta-baci a kan tsaro - Matasan arewa ga Buhari

- Kungiyar matasan arewa ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kaddamar da dokar ta-baci kan lamarin tsaro a yankin arewacin kasar

- Alhaji Yerima Shettima, shugaba kungiyar ya ce akwai bukatar sanya dokar ta-bacin duba ga yadda ake cigaba da kai hare-haren kan yankin duk da kokarin da sojoji ke yi na kawo karshen ta’addanci

- Shettima ya bukaci gwamnatin tarayya da ta yi gyara a tsarin tsaro domin samun damar magance kalubalen tsaro a arewa da sauran yankunan kasar

Kungiyar matasan arewa ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kaddamar da dokar ta-baci kan lamarin tsaro a yankin arewacin kasar.

Shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Yerima Shettima, ya ce akwai bukatar sanya dokar ta-bacin duba ga cigaban hare-haren da ake kai wa kan yankin duk da kokarin da sojoji ke yi na kawo karshen ta’addanci.

Yerima, wanda ke martani ga jawabin shugaban kasa Muhammadu Buhari na sabuwar shekara, ya yi zargin cewa matsalolin tsaro a arewa ya yi nisa da batun zuwa karshe sannan cewa akwai bukatar sabon dabara.

KU KARANTA KUMA: APC bata taba tunanin tsayar da Buhari a karo na uku ba – Gwamnan Nasarawa

Shettima ya bukaci gwamnatin tarayya da ta yi gyara a tsarin tsaro domin samun damar magance kalubalen tsaro a arewa da sauran yankunan kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel