Dan kasuwa a Kano ya bawa asibitin koyarwa kyautar na'urorin duba lafiya na miliyan N300

Dan kasuwa a Kano ya bawa asibitin koyarwa kyautar na'urorin duba lafiya na miliyan N300

Wani dan kasuwa a jihar Kano ya bawa asibitin koyar wa na jami'ar Ahmadu Bello (ABUTH) dake garin Zaria kyuatar wata na'ura da kudinta ya kai miliyan N300.

Da yake sanar da karbar tallafin na'urorin, babban darektan asibitin, Farfesa Ahmed Hamidu, ya bayyana cewa samun na'urar zai taimka matuka wajen kawo karshen wasu kalubale da asibitin da ya dade yana fuskanta wajen gudanar da aikinsa da duba lafiyar jama'a.

Farfesa Hamidu ya kara da cewa, duk da wanda ya bayar da tallafin ya bukaci a boye sunansa, ya zamar masa wajibi ya sanar da jama'a irin wannan aikin alheri da mutumin ya yi.

"Asibitinmu ya dade yana fuskantar kalubale masu yawa dake bukatar agaji daga bangarori da dama.

"Idan baku manta ba, ko yayin ziyarar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, sai da sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, ya nuna damuwarsa a kan irin yanayin da asibitin ke ciki tare da mika kukansa wurin shugaban kasa. Yanzu mun fara ganin abubuwan alheri suna faru wa," a cewarsa.

Dan kasuwa a Kano ya bawa asibitin koyarwa kyautar na'urorin duba lafiya na miliyan N300
Asibiti
Asali: UGC

A cewar Farfesa Hamidu, wanda ya bayar da tallafin ya sayi na'urorin ne a kan Dirham miliyan 2,659,912.50 wanda suka kama kusan miliyan N300 a kudin Najeria.

DUBA WANNAN: An binne yaro matashi da ransa a cikin wani kango a Kano - Kwamishinan 'yan sanda

Na'urorin, a cewarsa, sun hada da 'Flouroscopy Machines', na'urar wankin koda (Dialysis Machines) guda biyar, Computed Radiography X-ray, D10/Convex & Virginal Probes, ICU Ventilator AJ-2208, Mobile X-Ray Machine Mediaray, Ultrasound Machines da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel