Dadiyata: Iyali sun garzaya Kotu, sun bukaci a karbi N50m a hannun DSS

Dadiyata: Iyali sun garzaya Kotu, sun bukaci a karbi N50m a hannun DSS

A Ranar 2 ga Watan Agusta, 2019, wasu Mutane da ba a san su wanene ba, su ka sace Abubakar Idris (Dadiyata) daga gidansa cikin tsakar dare Garin Kaduna.

Daga wannan lokaci zuwa yanzu, kusan watanni buyar, ba a sake jin labarin inda wannan Bawan Allah da ya yi fice wajen sukar gwamnatin APC ya shige ba.

Domin ganin an dawo da Mai gidanta, Mai dakin wannan Matashin Malamin jami’ar tarayya da ke Dutsinma, Khadija Ahmad, ta shigar da DSS kara a kotu.

Khadija Ahmad ta na bukatar jami’an DSS da Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Kaduna, da gwamnatin jihar su fito da Mai gidanta ba tare da wata-wata ba.

Haka zalika Ahmed ta bukaci babban Lauyan gwamnatin Kaduna, ya biya Iyalin Dadiyata kudi Naira miliyan 50 saboda garkame shi da aka yi ba tare da hakki ba.

KU KARANTA: Kungiya mai zaman kanta ta yi tir da sace Dadiyata

Dadiyata: Iyali sun garzaya Kotu, sun bukaci a karbi N50m a hannun DSS
Dadiyata babban 'Dan adawan Gwamnati ne a kafafen sada zumuntan zamani
Asali: UGC

“Mu na neman kotu ta tursasa masu, su fito da shi, domin a doka babu wanda ya isa ya tsare mutum na sa’a 24 muddin akwai kotu.” Inji Muhammad Ismail Ashir.

Barista Muhammad Ismail Ashir shi ne Lauyan da ya tsayawa Iyalin Matashin da ake nema. Lauyan ya ke cewa su na kyautata zaton ya na hannun jami’ai.

Bisa la’akari da bayanan da mu ka samu, Mai dakinsa ta na ganin DSS ne su ke rike da shi a madadin gwamnatin Kaduna, don haka mu ke neman a sake shi.

A wannan takarda da Lauyoyi su ka sa hannu a madadin Iyalin Dadiyata, an bukaci wadanda ake karan su bada hakuri, sannan su guji sake cafke Malamin Jami’ar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng