Sababbin fasahohin zamanin da aka gani a Duniya daga 2010 - 2019

Sababbin fasahohin zamanin da aka gani a Duniya daga 2010 - 2019

Yayin da shekarar 2019 wanda ita ce ta karshe a shekaru goman farko bayan shigowar 2010, ta ke zuwa karshe, Farfesa Foluso Ladeinde, ya lissafo wasu cigaba da aka samu a shekarun.

Foluso Ladeinde fitaccen Malami ne wanda ya kan koyar a makarantar sojojin saman kasar Amurka, kuma ya na aiki a wani dakin binciken kimiyya da fasaha na tarayyan Amurka.

Ko da ba a samu wasu kirkire sosai a wannan shekaru ba, amma daga 2010 zuwa yanzu ne aka kara gyara dandulan Tuwita da WhatsApp, aka kuma dawo da manhajar da ke gane fuska.

Cigaban da aka samu ta fuskar kimiyya da fasaha daga 2010 kawo yanzu a Duniya sun hada da:

1. Wayar Samsung kirar Galaxy Note

A shekarar 2011 ne kamfanin Samsung su ka fito da wayar nan ta Galaxy Note mai babbar fuska da kuma karan alkalami. Daga nan ne irinsu Apple, HTC, LG, Motorola su ka ari wannan basira.

2. IPad

Wayar IPad ta na cikin manyan fasahar da aka gani a ‘yan shekarun nan da za su wuce yau. A Afrilun 2010 kamfanin Apple ya shigo da na’urar IPad mai fadin fuska fiye da sauran salula.

3. Instagram

A watan Oktoban shekarar 2010 ne aka fara amfani da dandalin Instagram a Duniya. A shekarar 2012 kuma Facebook su ka saye manhajar. A kan yi amfani da Instagram wajen wallafa hotuna.

KU KARANTA: Hukunci 10 da Alkalan kotu su ka yi da ya bada mamaki a 2019

4. SnapChat

A 2011 ne aka samu wasu tsofaffin ‘Daliban jami’ar Stamford ta Ingila da su ka kirkiro Snapchat bayan an yi Instagram. Evan Spiegel, Bobby Murphy, da Reggie Brown su ka yi wannan aiki.

5. Siri da Alexa dsr

Duk a shekarar 2011 ne kuma kamfanin Apple su ka kawo wani mutum-mutumi mai suna Siri a wayarsu ta iPhone 4S a lokacin. Mutum zai iya ba wannan manhaja ta Siri umarni da baki, kuma ta fahimta, ta yi abin da ake bukata. Daga baya aka shigo da Alexa da Amazon Echo a 2014.

Google su ma sun yi irin na su mutum-mutumin a 2016 bayan Microsoft sun kirkiro Cortana.

6. Air pods

A 2016 ne kamfanin Apple su ka sake nuna bajinta, su ka shigo da na’urar sauraron sauti a cikin kunnuwa maras amfani da zaren waya. Wasu su na ganin an kure basira a wannan na’urar.

7. Uber

A 2011 aka kirkiro fasahar nan ta Uber a Amurka. Kasashe da-dama kan yi amfani da motoci da sauran abubuwan hawan Uber wajen zirga-zirgar haya ko kuma bada sako da sauransu.

8. 4G

Kafin shekarar 2010, ba a fara amfani da tsarin 4G ba a Duniya. Wannan fasana na hawa yanar gizo na 4G shi ne ya gaji 3G a 2011. Wannan tsari ya na ‘dan karen sauri kamar yankan wuka.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng