Dan majalisar dokokin Sokoto ya mutu bayan ya yanke jiki ya fadi a majalisa

Dan majalisar dokokin Sokoto ya mutu bayan ya yanke jiki ya fadi a majalisa

Rahoton da ke zuwa mana ya nuna cewa Allah ya yiwa dan Majalisar dokokin jihar Sokoto, Honarabul Isa Harisu Kebbe, rasuwa.

Dan majalisar mai wakiltar karamar hukumar Kebbe ya rasu ne a yau Litinin, 30 ga watan Disamba.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa margayin ya yanke jiki ne ya fadi a majalisa inda a nan take ya amsa kiran mahaliccinsa.

An tabbatar da mutuwarsa bayan an kai shi asibitin koyarwa na Usman Danfodio.

Isa Harisu, wana ya kasance dan siyasa mai kwazo ya rike mukamai da dama a gwamnatin jihar Sakkwato ciki har da mai bai wa gwamna shawara kafin ya shiga zauren majalisa, kwarewarsa a harkar mulki ya sanya jam’iyarsa ta APC ta nemi ya tsaya takarar kujerar mataimakin Kakakin majalisar dokokin jiha in da ya sha kasa hannun wanda ke rike da kujerar yanzu Aminu Magaji na jam’iyyar PDP.

A wani labarin kuma, mun ji cewa Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana rashin amincewar al’ummar Musulmai da kudurin dokar daidaita maza da mata a kan abin da ya danganci rabon gado.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: FG ta takaita wa ministoci da wasu zuwa kasashen waje

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito Sultan ya bayyana kudurin dokar a matsayin abin da ya saba ma dokokin addinin Musulunci, don haka Musulman Najeriya ba zasu taba amincewa da ita ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel