Tor Tiv: Ka sa George Akume ya shiga taitayinsa – TYO ta fadawa Buhari

Tor Tiv: Ka sa George Akume ya shiga taitayinsa – TYO ta fadawa Buhari

Kungiyar Tiv Youth Organization wanda aka fi sani da TYO a jihar Benuewai ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jawo hankalin Sanata George Akume.

Wannan kungiya mai zaman kanta ta nemi shugaba Muhammadu Buhari ya yi maza ya sa George Akume ya shiga cikin taitayinsa a sakamakon zagin Sarkin Tibi da ya yi.

TYO a wani jawabi da ta fitar a jiya Ranar Lahadi 29 ga Watan Disamba, 2019, ta zargi Ministan kasar da laifin zagin Mai martaba Tor Tiv, watau Farfesa James Ayatse, kwanaki.

A cewar TYO ta bakin shugabanta, Timothy Hembaor, Akume ya yi kalamai masu zafi na cin mutunci game da Sarkin Tibi, inda ya zarge shi da nuna banbancin ra'ayin siyasa.

Kungiyar ta ce ba a nan kawai tsohon gwamnan jihar Benuwan ya tsaya ba, ta kai ya soki addini ta hanyar caccakar cocin da Mai martaba Sarkin kasar Tibin ya saba zuwa ibada.

KU KARANTA: Buba Galadima ya roki Buhari ya nada shi Shugaban INEC

Tor Tiv: Ka sa George Akume ya shiga taitayinsa – TYO ta fadawa Buhari

Tsohon Gwamna George Akume ya fadi zaben komawa Sanata a APC
Source: UGC

Mista Timothy Hembaor ya ce Ministan ya kira coci da Marasa tasiri saboda ba su da wani karfi a siyasa. Wannan ya sa kungiyar ta nemi shugaban kasa ya gargadi Ministan na sa.

“Mu a matsayinmu na Matasan kasar Tibi, mu na ganin kalaman da Sanata Akume ya furta a game da Sarkin Tibi da daukacin gidajen sarautun gargajiya matayin sabo, abin kunya, kuma abin da ba za mu yarda da shi ba, daga bakin Mutumin da jihar Benuewai ta haifa."

TYO ta ce: “Ba wannan ne karon farko da Akume ya jefi Sarkin Tibi Mai daraja da sauran manyan kasar. Akume bai kyale kowa; babba da yaro daga sukarsa ba tun da ya sha kasa a yunkurin sake komawa Majalisar dattawa, yanzu ya koma kan Mai martaba Sarki”

“Don haka mu na kiran shugaba a Muhammadu Buhari ya yi maza ya ja hankalin Ministansa, Wannan ne karon karshe da Akume ko wani zai labe da rigar siyasa ya ci mutuncin wani Sarki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel