Hotunan karramawar da Mai Mala Buni ya karrama Ahmad Lawan

Hotunan karramawar da Mai Mala Buni ya karrama Ahmad Lawan

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ahmad Ibrahim Lawan, ya samu babbar karramawa daga gwamnatin jihar Yobe.

Gwamna Mai Mala Buni shi ne ya karrama shugaban majalisar kasar a Ranar Asabar Disamba, 28 ga Watan Disamban 2019.

An shirya wannan liyafa ne a jiyaAsabar da ta gabata a cikin gidan gwamnatin jihar Yobe da ke babban birnin Damaturu.

Tsohon gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Gaidam shi ne shugaban gudanar da wannan karramawa da aka yi Sanatan na Yobe.

KU KARANTA: Wasu manyan Attajiran Arewa da ake ji da su a Najeriya

Hotunan karramawar da Mai Mala Buni ya karrama Ahmad Lawan

Mai Mala Buni da Danmasanin Bade Sanata Ahmad Lawan
Source: Twitter

Karamin Ministan harkar ayyuka da gidaje, Abubakar Aliyu, ya na cikin wadanda su ka shiryawa Sanatan wannan biki.

Ahmad Lawan shi ne mai wakiltar Arewacin jihar Yobe a majalisar dattawa. Tun 2007 aka zabe shi a matsayin Sanata.

A 2003, Ahmad Ibrahim Lawan, ya fara wakiitar Yankin Yobe a majalisar wakilai a karkashin jam’iyyar adawa ta ANPP.

Sanatan ya yi magana a shafin Tuwita bayan wannan biki da aka shirya masa, inda ya nuna cewa ya yi farin cikin ranar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Online view pixel