Faduwar wasu ce ta zo ba ta Kannywood ba – Naziru Sarkin waka

Faduwar wasu ce ta zo ba ta Kannywood ba – Naziru Sarkin waka

Shahararren mawakin nan na masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood kuma Sarkin wakar sarkin Kano, Naziru M Ahmad, ya karyata jita-jitan cewa kamfanin shirya fina-finan na shirin durkushewa.

A cewar Naziru karshen wasu ne ya zo, amma suke ganin karshen masana’antar ce ta zo.

Har ila yau ya kara da cewa zamani ne ya kayr da wasu, idan aka yi la’akari da yadda masana’antar take a baya da yanzu, mafi akasarin masu shirya fina-finai na zamanin nan sun kasance ba a bakin komai ba a baya.

Daga karshe ya ce dama can an kafa masana’antar ne babu shugabanci, kamar an gina ne aka share fili aka dora. Saboda haka wasu ma nan gaba za su kawo irin nasu tsarin a haka za a yi ta tafiya.

A wani labarin kuma, mun ji cewa Zulaihat Ibraheem jaruma ce da aka fi sani da ZPreety. Jaruma ce da bata dade da shigowa masana’antar Kannywood ba amma ta samu daukaka mai tarin yawa. Ba a fim kadai ta tsaya ba, ta kasance tana yin gajerun bidiyon ban dariya inda take wallafa su a shafinta na Instagram.

KU KARANTA KUMA: An kama wani saurayi da ya dane tayar jirgin sama a lokacin da yake shirin tashi a filin jirgin sama na Legas

Hakan kuwa ya sa tayi farin jini da karin suna. Kamar yadda jarumar ta bayyanawa jaridar Fim Magazine, an haifeta ne a 1997 kuma ‘yar asalin jihar Kebbi ce daga kauyen Rubba dake karamar hukumar Dankuwa. Don haka asalin iyayenta Dakarkari ne a yankin Zuru.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel