Hotuna: Dan sanda ya yiwa matarsa dukan kawo wuka kan N500 a Kaduna

Hotuna: Dan sanda ya yiwa matarsa dukan kawo wuka kan N500 a Kaduna

- Hoton wata matar dan sanda jina-jina ya ja hankulan mutane a kafafen sada zumunta

- An zargi dan sandan mai suna Sajan Yusuf Bello, da yi wa matarshi dankaren dukan a kan N500

- Kwamishinar walwala ta jihar Kaduna ta sha alwashin bin diddigi tare da daukar mataki a kan mijin

Wata mata wacce har yanzu ba a gano sunanta ba ta jawo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani sakamakon hotunanta face-face cikin jini da ke yawo.

Kamar yadda ake zargi, mijin matar dan sanda ne ma’aikaci a jihar Kaduna. Dan sandan ya yi wa matarshi mugun duka ne a kan dan hargitsi da suka samu akan naira dari biyar.

Mijin da aka gano sunansa da Sajan Yusuf Bello yayi wa matarshi jina-jina ne bayan da suka yi fada a kan wannan kudin.

Hotuna: Dan sanda ya yiwa matarsa dukan kawo wuka kan N500 a Kaduna

Hotuna: Dan sanda ya yiwa matarsa dukan kawo wuka kan N500 a Kaduna
Source: Facebook

A yayin mayar da martani a kan wannan cigaban, kwamishinar walwalar jama’a ta jihar Kaduna, Hafsat Baba ta wallafa wannan labarin a yanar gizo. Ta yi alkawarin gano jami’in dan sandan tare da ladabtar da shi.

Hotuna: Dan sanda ya yiwa matarsa dukan kawo wuka kan N500 a Kaduna

Hotuna: Dan sanda ya yiwa matarsa dukan kawo wuka kan N500 a Kaduna
Source: Facebook

Kamar yadda kwamishinar ta wallafa a shafinta na tuwita, “na lura cewa wannan lamarin ya fara yawaita. Jami’an tsaro na jin kamar sun fi karfin hukuma. Ina kira ga hukumar ‘yan sandan Najeriya da sauran jami’an tsaron da abun ya shafa, da su dauki matakin gaggawa.

KU KARANTA: Na koma Legas da zama ne saboda na ceci rayuwata - Adam A Zango

“Mun kai koken mu ga ma’aikatar tsaron cikin gida a karkashin Samuel Aruwan. Muna da tabbacin za a dau mataki a kan wannan lamarin. Amma kuma, akwai bukatar mu tattauna a kan daililin wannan cin zarafin da mata ke fuskanta a gidajen aurensu.

“Abun na cin min tuwo a kwarya ta yadda wannan mijin ya yi wa matarshi. Wannan Sajan Yusuf Bello din ya yi wa matar shi duka ne a kan N500. Ina soyayya da mutunta junan dake tsakanin mata da miji suka tafi?”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel