Ayyiriri: Jaruma Halima Atete ta kusa zama amarya
Sananniyar jaruma Halima Yusuf Atete za ta zama amarya a watan Janairu mai zuwa na shekarar 2020, wata kwakwarar majiya ta tabbatar wa da mujallar fim.
Ba tun yau ba ake maganar auren jarumar, amma sai magana ta kankama sai kuma a ji ta yi sanyi. Idan aka tuntubeta da zancen, sai ta ce ba haka abin yake ba, tana jiran lokacin auren nata ne.
A cikin kwanakin nan kuwa, sai zancen auren jarumar ya kara tasowa gadan-gadan, ya yadu a cikin masana'antar fina-finan. Labarin ya sake samun karfi ne ta yadda aka ga 'yan uwanta jarumai na dora labarin a shafukan su na Intagram.
Duk da yaduwar labarin a kafafen sada zumuntar zamani, babu wani makusancinta da ya fito ya karyata lamarin.
Mujallar fim ta yi ta kokarin jin ta bakin jarumar, amma hakan bai yuwa ba saboda bata daga wayarta da aka dinga kira ba. Hakazalika bata mayar da martanin sakonnin kar-ta-kwana da aka yi mata ba.
DUBA WANNAN: Ina wasan kwaikwayo, ina siyasa - Rukayya Dawayya
Amma daya daga cikin makusantan amarya Halima Atete, ya tabbatar da gaskiyar lamarin. Ya kara da cewa, dage auren aka yi amma da yanzu haka an riga anyi.
Ya ce, "An shirya yin auren a wannan watan na Disamba amma saboda wasu dalilai sai aka mayar dashi zuwa watan Janairu na sabuwar shekara."
Da mujallar ta tambayesa ko wanene angon Halima, sai ya ce, "Har yanzu babu wanda zai iya fada maka wanda Halima zata aura, domin kuwa hasashe kawai ake ta yi. Amma mafi karfin magana ita ce, ana zaton zata auri wani mawaki ne mai suna Isiyaku Ferus, mawakin siyasa ne. Ya yi tashe wajen wake Shugaba Buhari da APC. Shi ne aka fi sani suna soyayya da jarumar tsawon lokaci, kuma soyayyar tasu ba boyayya bace."
Ya kara da cewa, "A tsawon zamanta a Kannywood, babu wanda aka taba ganin ta bayyana soyayyarsa a fili kamarsa. Don haka ne aka fi kyautata zaton shi ne angon na Halima Atete."
Ko ma dai waye kuma ko mene ne, rana bata karya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng