Boko Haram sun yi yunkurin shiga cikin babban birnin Jihar Yobe

Boko Haram sun yi yunkurin shiga cikin babban birnin Jihar Yobe

Dakarun Sojojin Najeriya sun bayyana cewa sun takaita wani harin ‘Yan ta’addan Boko Haram a babban birnin jihar Yobe na Damaturu a Ranar Lahadi.

Kamar yadda mu ka samu rahoto dazu, Jami’an tsaron sun yi nasarar dakile wannan hari na Boko Haram ne a jiya Ranar 22 ga Watan Disamba, 2019.

Jaridar Premium Times ta ce Bayin Allah sun tsere sun shiga cikin gidajensu a lokacin da aka fara kai wannan hare-hare a yammacin Ranar Lahadi.

Jami’in Soja da ke magana da yawun Operation Lafiya Dole, Damaturu, Njoka Irabor, ya shaidawa ‘yan jarida cewa sun takawa duk ‘Yan ta’addan burki.

“Yan ta’addan sun nemi shiga Damaturu ta yankin Arewacin Garin, amma Sojojin kasa da na sama su ka yi la-las da su.” Inji Kyaftin Njoka Irabo.

KU KARANTA: Boko Haram sun kai hari a Jihar Borno sun kashe Ma'aikata

Boko Haram sun yi yunkurin shiga cikin babban birnin Jihar Yobe
Sojoji sun takawa Boko Haram burki.a Damaturu
Asali: Facebook

Yayin da ake wannan ba-ta-kashi tsakanin ‘Yan ta’addan da Sojoji, an rufe hanyar shiga Garin, wannan ya sa jama’a su ka makale a kan titi.

Daga cikin wadanda su ka yi carko-carko a hanya bayan an garkame babban titin shiga Garin na Damaturu, har da Tawagar motocin gwamnan jihar.

Legit.ng ta tuntubi wasu daga cikin Mazauna Garin Damaturu, inda aka shaida mata cewa abubuwa sun lafa saboda kokarin Dakarun Soji.

Da kimanin karfe 8:30 na daren jiya, wani Matashi ya bayyana mana cewa jirgin yakin Sojojin saman Najeriya ya na ta faman shawagi a sama.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel