Yadda wani mutum ya kwakule idon yarinya mai shekaru 4

Yadda wani mutum ya kwakule idon yarinya mai shekaru 4

Jami'an 'yan sanda a jihar Taraba sun kai samame tare da cafke wani gagarumin matsafi. Matsafin na amfani da sassan jikin mutane ne don cikar aikinsa. Bayan kwakule idon yarinya mai shekaru hudu a duniya ne asirinsa ya tonu.

Wanda ake zargin mai shekaru 38 mai suna Jumpi Bako, ya shiga hannu ne bayan da aka zargesa da kwakule idon wata yarinya mai shekaru hudu mai suna Sunkuni, kamar yadda gidan talabijin din Channels ya ruwaito.

Jami'an tsaro sun cafke Jumpi Bako a karamar hukumar Ardo-Kola dake jihar Taraba.

Jami'an 'yan sandan sun bayyana cewa, sun tseratar da yarinyar amma tana cikin mawuyacin hali, kuma an garzaya da ita asibiti don karbar taimakon gaggawa.

Sauran shaidun da aka samu daga wanda ake zargin sun hada da bindiga kirar Ak-47 wacce ake zargin yana amfani da ita ne wajen harar mutane.

DUBA WANNAN: Marin dan majalisa: Majalisar jihar ta bukaci a cafko shugaban karamar hukuma

A yayin jawabi ga manema labarai, kwamishinan 'yan sandan jihar, Alkasim Sanusi, ya ce hukumar ta cafke wasu mutane biyu da take zargi da garkuwa da tsohon shugaban ma'aikatan gwamnatin tsohon gwamna Danbaba Suntai, Alhaji Aminu Jika.

Shugaban 'yan sandan ya ce, an samu damar yin wannan kamen ne sakamakon hadin guiwar jami'ansu da mafarauta da kuma 'yan kungiyoyin sa kai.

An kara da kama wani Ibrahim Jafaru, shugaban kungiyar masu satar motoci da suka addabi babban birnin jihar na Jalingo.

Kamar yadda CP Sanusi ya ce, bincike ya nuna cewa wadanda ake zargin sunyi nasarar satar ababen hawa 35 daga watan Janairu 2018 a garin Jalingo, jihar Taraba. Suna kuma kai motocin tare da siyar dasu a jihohin fadin kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel