A shirye nake ga duk mutumin da yake bukatar aurena - Rahama Sadau

A shirye nake ga duk mutumin da yake bukatar aurena - Rahama Sadau

- Bayan bikin murnar zagayowar ranar haihuwar jaruma Rahama Sadau, ta bude katafaren kamfaninta dake Kaduna

- Jarumar ta bayyana cewa ita fa ko yanzu mai son aurenta ya shirya, ta yazo kuwa ya dauka

- Ta bayyana cewa, babu wani abu dake tsakaninta da jarumi Sadiq Sani sadiq duk da hotunansu da aka gani kamar na aure

A ranar 10 ga watan Disamba ne jaruma Rahama Sadau ta yi bikin zagayowar ranar haihuwarta. A hakan ne kuma ta bude sabon katafaren gidan cin abinci, wajen kwalliya, wajen gyaran jiki, wajen gyaran kai da kuma wajen shan Shisha wadanda ta kira da ‘Sadau Homes’.

Bayan nan ne jarumar ta samu zantawa da jaridar Fim Magazine inda ta amsa mata wasu tambayoyi masu matukar muhimmanacin.

A lokacin da jaridar ta tambaya jarumar yadda take ji a kan sukarta da mutane keyi, tace ita bata san suna yi ba. Saboda mutane ne ke ji ba ita ba. Sam ita bata sauraron cece-kuce din mutane.

An bukaci jin ta bakin jarumar a kan abinda ke tsakaninta da jarumi Sadiq Sani Sadiq, sakamakon hotunan da aka gani nasu kwanakin baya suna ta yawo kamar na shirin aure.

KU KARANTA: Tirkashi: Shugaban kasar Zambiya ya yiwa jakadan Amurka korar kare bayan yayi magana kan Luwadi

Jarumar ta ce, “Babu wata soyayya da ta wuce ta ‘yan uwantaka tsakanina da Sadiq. Wadannan hotunan kuwa na wani Fim ne da muka yi. Fim din kuwa tuni ya fita don mutane sun ganshi.”

Da aka tambaya jarumar yaushe zata yi aure? Sai tace “Ko yanzu mai sona ya fito a shirye nake, ya zo ya dauka.”

Jarumar ta bayyana cewa, a halin yanzu tafi fitowa a fina-finan kudancin kasar nan fiye da na Kannywood. Kuma bata saka lokacin barin shirin Fim ba gaskiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel