Wanene Marigayi Sanata Benjamin Chukwuemeka Uwajumogu?

Wanene Marigayi Sanata Benjamin Chukwuemeka Uwajumogu?

A Ranar 18 ga Watan Disamba, 2019, aka ji labarin cewa Benjamin Chukwuemeka Uwajumogu, ya cika. Kafin rasuwarsa, shi ne Sanata mai wakiltar Arewacin jihar Imo a majalisar dattawa.

Mun tsakuro maku kadan daga cikin tarihin wannan ‘Dan majalisa. Ga kadan daga ciki:

1. Rayuwa

An haifi Benjamin Uwajumogu ne a ranar karshe na watan Yuni a shekarar 1968 a Garin Umuihi Ihitte da ke cikin karamar hukumar Uboma a yankin Okigwe da ke jihar Imo a Kudancin Najeriya. Sanatan ya auri Misis Elleen Uwajumogu wanda ta haifa masa ‘Ya ‘ya uku kafin ya bar Duniya.

2. Karatu

Marigayin ya soma karatu ne a gida har ya tafi mataki na gaba da Sakandare. Ya yi Digiri a Jami’ar New Jersey da ke Amurka a 1986. Ya kuma yi wasu kwas a irinsu babbar jami’ar nan ta Schiller da ke Birnin Faris a kasar Faransa. Ya kuma halarci wata jami’ar Sorbonne da ke Faransa.

3. Siyasa

Tun Ben Uwajumogu ya na ‘Dan shekaru 20 da ‘yan kai a Duniya ya shiga siyasa. A 1991 ne ya rike shugaban jam’iyyar SDP na karamar hukumarsa bayan an dawo siyasar farar hula a Najeriya.

KU KARANTA: Wani Sanatan jihar Imo ya riga mu gidan gaskiya

A 2011 ya zama Kakakin majalisar dokokin jihar Imo a lokacin Rochas Okorocha ya na gwamna. A 2017 ya yi sa’ar tafiya majalisar dattawa bayan ya yi irin wannan yunkuri a 2015 ya sha kasa.

Uwajumogu ya zarce a kan kujerar Sanata a zaben 2019, ya doke Athan Achonu na jam’iyyar PDP.

Da ya ke Kakakin majalisar Imo, Ben Uwajumogu ya yi ikirarin kawo dokoki 31 da kudiri fiye da 130 da za su taimakawa jiharsa. A cewarsa, ya kuma sa an yi tituna da makarantu a Kauyensa.

Sanatan ya kuma ce ya samawa Matasa 900 a lokacin da yake Kakaki a jiharsa. Watakila wannan ya sa Ahmad Lawan ya nada shi shugaban kwamitin kwadago a majalisar dattawa mai-ci.

Marigayin ya na cikin ‘Yan-autan Sanatocin da ke majalisa a shekaru 51. Bayan haka kuma yana cikin Sanatoci 3 da APC ta ke da su daga Kudu maso Gabashin Najeriya a majalisar da ta shude.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel