Zan fara shiga aji na koyar da darasi a makarantu - Shugaban karamar hukuma

Zan fara shiga aji na koyar da darasi a makarantu - Shugaban karamar hukuma

- Shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa, Alhaji Ado Tambai Kwa ya ce zai fara koyarwa a zangon karatu na gaba

- Ado Tambai Kwa yace zai fara koyar da darasin Physics ne da lissafi a makarantun gwamnatin karamar hukumar

- Ya bayyana yadda gwamnatinshi ta siya motoci masu mazaunin mutane 50 guda uku don kaiwa da kawowar ‘yan makaranta

Shugaban karamar hukumar dawakin Tofa, Alhaji Ado Tambai yace daga zangon karatu mai kamawa, zai fara koyarwa a makarantun yankinshi da ‘yan majalisar shi.

Ado Tambai Kwa ya fadi hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da filin Barka da Hatsi na gidan rediyon Freedom da ke Kano.

Da aka tambayi Ado Tambai ko me zai koyar a zangon karatun mai kamawa, sai yace, zai iya koyar da darasin Physics da darasin lissafi tunda shi Injiniya ne.

Ya ce, tun bayan da aka rantsar dashi a matsayin shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa, ya bayar da karfi wajen fannin habaka ilimi a yankin.

KU KARANTA: A karon farko Baballe Hayatu yayi magana akan abubuwan da suke haddasa rikici a Kannywood

Ado Tambai Kwa ya ce, akwai yara da dama da basa iya zuwa makaranta sakamakon rashin abun hawa da kuma rashin karfin iyayensu.

Ya tabbatar da cewa, hakan ne ya sa ya siya motoci guda uku masu mazaunin mutane 50 domin kaiwa da kawowar yara daga makaranta.

A bangaren kudaden shiga kuwa, ya ce lokacin da ya karbi ragamar shugabancin karamar hukumar, ya ce naira dubu dari da hamsin kacal suke samu. Amma a halin yanzu suna samun kimanin naira miliyan uku ko fiye da haka a duk wata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel