Cin barkono yana kare mutane daga mutuwa ta hanyar bugun zuciya - Bincike

Cin barkono yana kare mutane daga mutuwa ta hanyar bugun zuciya - Bincike

- Dadin barkono ya wuce kawai a baki, yana da wasu amfani masu yawa, kamar yadda bincike ya nuna

- An fara wannan binciken ne a kasar Italiya, inda aka gangara har kasar China da Amurka

- Cin barkono na rage yuwuwar mutuwa ta sanadin ciwon zuciya ko shanyewar bangaren jiki na raguwa

Dadin barkono ya wuce kawai a baki, yana da wasu amfani masu yawa, kamar yadda bincike ya nuna.

Tun shekaru aru-aru da suka gabata, an gano cewa barkono yana da wasu sinadaren magunguna da ke kunshe a ciki. A hali yanzu kuwa, ma’abota bincike sun gano cewa, cin barkono na rage yuwuwar mutuwa daga ciwon zuciya da shanyewar bangaren jiki.

Binciken da aka yi a kasar Italiya, inda barkono ya zamo sinadarin girki gama-gari, binciken ya danganta yuwuwar mutuwa tsakanin mutane 23,000 wadanda suke cin barkono da wadanda basu ci.

An lura da yanayin cin abincin mutanen ne na shekaru takwas kuma masu binciken sun gano cewa raguwar yuwuwar mutuwar mutane masu cin barkonon ta ragu da kashi 40. Ta bangaren shanyewar barin jiki kuwa ya ragu da fiye da rabi, kamar yadda wata mujallar Amurka ta bayyana a ranar Litinin.

Bayan bincike a China da Amurka, an gano amfanin cin barkono a girki.

KU KARANTA: Tirkashi: Ango ya nemi a raba aurenshi da matarsa, bayan tana tsula masa fitsarin kwance a gado kullum

“A halin yanzu, kamar yadda muka gano daga binciken da muka yi a China Da Amurka, mun gano cewa barkono yana da matukar amfani a abinci. Duk da kuwa cewa, akwai yanayi daban-daban da ake cin shi a sassan duniya,” Lacoviello ya ce.

Duk da an gano wasu koma baya da binciken ya fuskanta, amma an jinjinawa wannan binciken. Masu binciken kuwa na kokarin gano dalilin da yasa barkonon ke da matukar amfani a jikin dan Adam.

Amma kuma, masu binciken sun gano cewa, komai kankantar barkonon amfaninshi daya. Babu wata bukata ta cin barkonon da yawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel