Zaben 2019: Sakamakon zabuka 10 da suka ba 'yan Najeriya mamaki

Zaben 2019: Sakamakon zabuka 10 da suka ba 'yan Najeriya mamaki

Duk da cewa zaben 2019 ya zo ya tafi, abubuwan mamaki da yawa sun faru a lamurran siyasar Najeriya. A kowanne zabe a duniya, jam’iyyun siyasa da magoya bayan su ne suke kara karfin guiwa a karshen zaben, daga nan kuma ake gane wanda ya yi nasara da wanda ya fadi.

Ba wai abubuwan mamaki kadai zaben ya zo dasu ba, har da abubuwan al’ajabi ta yadda karfin ikon wasu ‘iyayen gida’ ya dinga karewa.

Wani abun mamakin shine yadda aka dinga maka sanatocin da suka canza sheka daga APC zuwa PDP tare da tsohon shugaban dattawa kasa.

A wannan rubutun, legit.ng ta tattara manyan masu nasara a zaben 2019 da manyan wadanda suka sha mugun kaye a zaben 2019.

1. Bukola Saraki

Kafin ya sha kaye a zaben ranar 23 ga watan Fabrairu, tsohon shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya kasance mutum mai matukar rinjaye kuma ubangida ne a siyasar jihar Kwara. Tsohon gwamnan jihar Kwara ne daga shekarar 2003 zuwa 2011, kafin a zabesa don wakiltar jihar Kwara ta tsakiya a karkashin jam’iyyar PDP.

Bayan ya sake komawa majalisar dattijai a 2015, Saraki ya canza sheka zuwa jam’iyyar PDP. Lamarin da ya jawo tashin-tashina a majalisar dattijan, don kuwa ya canza sheka ne tare da wasu sanatocin ana sauran watanni kalilan zaben 2019. An maka sanatan da kasa a yayin zaben 2019 din.

2. Godswill Akpabio

Tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom ne kuma ubangidan siyasar jihar mai albarkatun man fetur. Ya canza sheka daga PDP zuwa APC kuma ya sha kayen yunkurin komawa majalisar dattijan. Amma ya samu sa’a don an nada shi ministan lamurran Neja Delta don wanke masa zafin kayen da ya sha.

DUBA WANNAN: Jam'iyyar APC ta yi ta'aziyar rasuwar tsohon mataimakin shugabanta na kasa

3. Rabiu Kwankwaso

Tsohon gwamnan Kano ne kuma ubangidan siyasar jihar Kano. Bai nemi komawa majalisa ba, amma ya nemi tikitin takarar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar PDP. Atiku Abubakar ne ya samu cafke tikitin.

4. George Akume

Tsohon gwamnan jihar Benuwe din ya sha mugun kaye ne a yayin da suka gwabza neman kujerar komawa majalisar dattijai da Orkev Jev na jam’iyyar PDP.

5. Shehu Sani

Mai rajin kare hakkin bil Adama din da ya koma dan siyasa, ya canza daga jam’iyyar APC zuwa PRP saboda rashin samun tikitin takara a APC. Ya sha bakin kaye a hannun Uba Sani wanda makusanci ne ga Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna.

6. Dino Melaye

Wannan sanatan daga jihar Kogi ya canza sheka tare da Saraki daga APC zuwa PDP. INEC ta bayyana shi a matsayin mai nasara a zaben da aka yi. Smart Adeyemi ya garzaya kotu inda aka bukaci sauya zaben. Daga nan ne kuwa Adeyemi ya maka Melaye a kasa.

7. Abiola Ajimobi

Faduwar wannan tsohon gwamnan ta ba mutane mamaki. Dan takarar kujerar majalisar dattijai na jam’iyyar PDP ya maka shi da kasa. Duk da kuwa ba wani babbar tazara ce tsakanin Ajimobi da Balogun ba.

8. Yakubu Dogara

Tsohon kakakin majalisar wakilan Najeriya ne da ya canza sheka daga APC zuwa PDP ana sauran watanni kadan zabe. A tsammanin kowa, dogara zai sha kaye, amma sai gashi ya kada Dalhatu Kantana kasa warwas. Da hakan ya samu komawa majalisar tarayyar.

9. Aminu Tambuwal

Wannan nasarar ta ba ‘yan Najeriya mamaki ba kadan ba. Ya hau karagar mulkin jihar a APC amma sai ya sauya sheka zuwa PDP. A hakan kuwa ya yi nasarar komawa kujerarsa duk da rigingimun da ke tsakaninsa da ubangidansa na siyasa, Aliyu Wamakko.

10. Omoyele Sowore

Yana da kwarin guiwar zai lashe zaben shugabancin kasa a 2019 matukar an yi zaben gaskiya. Yana ikirarin cewa matasa na goyon bayansa, amma sai Shugaba Buhari ya yi masa warwas a zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel