Janar Babangida na nan da ransa, garau cikin koshin lafiya - Hadiminsa
Ana ta rade-radin cewa tsohon shugaban Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya ya mutu. An fara wannan jita-jita ne a safiyar Ranar Lahadi, 15 ga Watan Disamban 2019.
Kakakin tsohon shugaban na Najeriya, Kassim Afegbua, ya fito ya yi cikakken jawabi, ya na mai musanya wannan labari na cewa Ibrahim Babangida ya cika bayan ya yi fama da rashin lafiya.
Mista Afegbua a jawabin na sa da ya yi wa take da cewa ‘IBB na nan garau a raye’ ya ce: “Bini-bini yanzu a kan fito da labarin karya ana neman kirawa IBB wanda mu ke kira DON, mutuwa”
“Sabon kudirin da ke kokarin yakar labaran karya shi ne abin da zai yi maganin masu yada wannan labarai na karya. IBB na nan raye lafiya lau. Yanzu ya fara ganin mutane.” Inji Afegbua.
KU KARANTA: Faston ya ce Gwamnan Kaduna ba zai taba yin mulki a Najeriya ba
Mai magana a madadin tsohon shugaban kasar ya ce yanzu haka da ranar nan, IBB ya ke ganawa da ‘Yanuwa da Abokan arziki da su ka kai masa ziyara a katafaren gidansa da ke Minna Hilltop.
“Allah ya yafewa masu yi wa IBB fatan mutuwa. Ubangiji ne mai badawa kuma mai daukar rai, ba mutum ba. Mutuwa ce karshen da za ta samu kowane halitta ko ba jima ko ba dade wata rana.”
Hadimin ya kara da cewa: “Amma a rika yada labarin karya game da ajali, ana yi wa mutum fatar mutuwa, ya cika rashin sanin darajar ‘Dan Adam. Allah ya yafe masu yi wa IBB fatan mutuwa.”
“Wannan shi ne karo na uku da ake yi masa fatan mutuwa a bana, Idan Allah ya so sai IBB ya cika burinsa a Duniya. Mu na godewa wadanda su ka tuntube mu domin jin gaskiyar lamarin.”
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng