Kankanba: Amarya da ango sun kashe kansu a kan bashin biki

Kankanba: Amarya da ango sun kashe kansu a kan bashin biki

Wata budurwa ‘yar Najeriya wacce aka bayyana da suna Tola ta wallafa wani labara da ya ba mutane mamaki. Ta wallafa labarin ne a shafinta na kafar sada zumunta ta tuwita.

Tola ta wallafa labarin yadda wasu sabbin ma’aurata suka kashe kansu. An gano cewa, mugun bashin da suka ci ne yayin bikinsu ya jawo hakan. Bayan bikin, sai suka yanke shawarar kashe kansu, kowa ya huta.

Kamar yadda Tola ta wallafa a shafinta na tuwita, “Wasu ma’aurata sun kashe kansu bayan kwanaki uku da aurensu. Ma’auratan sun sha guba mai suna ‘snipper’ inda suka sheka lahira. A yau ne kwanaki bakwai da yin bikin,

DUBA WANNAN: Fasto ya yi wanka a coci, jama'a sun shanye ruwan

“Har yanzu ina cikin firgici. Ku zo mu koka tare. Wannan ne karo na farko da nake kuka a wannan shekarar. A lokacin da aka sanar, ban yadda ba har sai da na gani da idona. A halin yanzu suna ma’adanar gawawwaki.” Ta wallafa a shafinta na tuwita.

Amma kuma wani ma’aboci amfani da kafar sada zumuntar ta tuwita, ya nemi musanta zancen. Ya yi hasashen cewa akwai yuwuwar ba bashin biki bane yasa suka kashe kansu. Tola ta mayar da martani kamar haka, “Shi ne, bashin biki ne. 'Yan uwan mijin sun jaddada hakan don ya dinga maimaita hakan kafin rasuwarsa.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel