Mutumi zai yi zaman daurin shekaru 10 saboda satar Miliyan 25 ta yanar gizo

Mutumi zai yi zaman daurin shekaru 10 saboda satar Miliyan 25 ta yanar gizo

Babban kotun tarayya da ke Garin Legas ta samu wani Mutumi mai suna Jules Suinner da laifin damfara. Alkali ya tabbatar da cewa an same shi da laifin damfarar kudi har Naira miliyan 25.

Alkali mai shari’a Chuka Obiozor, shi ne ya yanke wannan hukunci a zaman da ya yi a Ranar Juma’a, 13 ga Watan Disamban 2019. Mista Suinner mutumin Najeriya ne da ke damfarar mutane.

Mai shari’an ya samu Jules Suinner da duka jerin laifuffuka shida da hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa ta ke tuhumarsa da su, kamar yadda mu ka samu labari.

EFCC ta fadawa kotu cewa Mista Jules Suinner ya yi wa sakonnin yanar gizon wani kamfani mai suna "Greenview Development Nigeria Limited" kutse, inda ya saci tambarinsu, ya tafka barna.

KU KARANTA: Mai saida wiwi ya tafi kotu bayan ya kirawa ‘Yan damfara ‘Dan Sanda

A cewar EFCC, wannan Mutumi ya yi amfani da takardar tambarin wannan kamfani ne wajen sace Naira miliyan 25 daga cikin asusun bankinsu, ya jefa su zuwa wani kamfanin ta yanar gizo.

Asusun kamfanin da aka aika wannan kudin sata shi ne "ICT Aid Foundation Cooperative Society." Bayan sauraron karar a kotu, Alkalin ya samu wannan mutumi da wannan danyen aiki.

“Na gamsu cewa labarin da wanda ya ke kare kansa ya bada katon kanzon kurege ne. Masu kara sun tababatar da cewa wanda ake tuhuma ya aikata duka laifuffukan da ake zarginsa da su.”

“Don haka an samu wanda ake kara da laifin duka zargin da ke wuyansa, a sakamakon haka za a daure shi.” Inji Alkali Obiozor. Wannan ya sa aka yanke masa daurin shekaru goma a kurkuku.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel