Tirkashi: Matashi mai shekaru 19 dirka wa mahaifiyarsa cikin shege

Tirkashi: Matashi mai shekaru 19 dirka wa mahaifiyarsa cikin shege

Wani matashi mai shekaru 19 ya yi wa mahaifiyarsa cikin shege sakamakon gwajin da ya yi na maganin soyaya da aka ba shi a kanta.

Lailasnews ta ruwwaito cewa yaron mai suna Ekanem ya karbo maganin soyayar ne daga hannun wani boka inda ya gwada a kan mahaifiyarsa da kuma daya daga cikin matan da ke kula da dalibai a makarantarsu ta kwana.

Lamarin ya faru ne a garin Fatakwal ta jihar Rivers yayin da mijin matar ya yi tafiya zuwa wata jihar wadda hakan yasa ya musanta cewa cikin ba nasa bane yayin da ya ke amsa tambayoyi.

Mahaifiyar yaron ta yi bayyani kamar haka: "Ban san yadda lamarin ya faru ba, abinda zan iya cewa kawai shine wani matashi mai kama da da na ya fado cikin daki na da asubahi kuma na kasa cewa ufan," ta kara da cewa ba za ta iya bayyanin yadda lamarin ya afku ba.

DUBA WANNAN: Me ya yi zafi? Amarya ta fada rijiya ana gobe bikinta a jihar Kano

Yaron da yanzu ya ke hannu a hedkwatan 'yan sanda ya ce, "Na yi matukar nadamar abinda ya faru, banyi niyyar haka ta faru ba. Kawai na ga na fara kaunar ta ne bayan da aka bani maganin soyaya.

"Dole in fadi gaskiya domin na san idan na yi hakan Allah zai sanyaya zuciyarta ta yafe min. Kwatsam na tsinci kai na ina saduwa da mahaifiya ta yayin da na ke tunanin maganain ba zai yi aiki ba. Bayan haka na yi barazanar zan kashe ta idan ta sanar da 'yan sanda abinda ya faru."

Mai magana da yawun yan sandan jihar, DSP Celestine Kalu ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce tuni an kama yaron kan laifin barazanar aikata kisar gilla.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel