Jerin kayan da su kara kudi da wadanda su ka yi sauki a kasuwa

Jerin kayan da su kara kudi da wadanda su ka yi sauki a kasuwa

Farashin kaya da-dama sun sauko kasa makonni bayan an samu hauhawar kayan masarufi a fadin kasar. Rufe kan iyakoki da aka yi ya na cikin abubuwan da su ka jawo tashin kudin.

Binciken da Nairametrics ta yi, ya nuna cewa shinkafar gida su na cigaba da shiga kasuwanni bayan an yi girbi. Wannan ya taimaka wajen raguwar farashin kayan abincin da ke kasuwanni.

A binciken kwanan nan da Nairametrics ta wallafa, mun fahimci cewa a kan samu buhun shinkafa a kasa da N17, 000 a yanzu. Bayan haka, farashin albasa da kuma tumatur sun karye.

Duk da wannan sauki da aka samu a cikin makonni biyun da su ka wuce, wasu kayan da aka saba amfani da su a yau da kullum sun tashi sama. Daga cikinsu akwai man gyada, da man ja.

KU KARANTA: Amarya ta burma cikin rijiya ana shirin bikin ta a Kano

Wasu kayan kasar wajen da yanzu su ka yi wahala ba su rage kudi ba. Bincike ya nuna cewa kara tsada ma wasu ke yi a halin yanzu. Akwai buhunan da yanzu farashin su ya kai akalla N26, 125.

Binciken ya nuna kwanon jan gari ya tashi daga N6, 125 zuwa N6, 250, wannan ya na nufin an samu karin 2.04%. Farashin litar man ja ya tashi sosai daga kusan N1, 800 zuwa fiye da N2, 000.

Man gyadan da ake yi a gida ya kara kudi da kashi 25%. Gorar lita 25 ta koma N13, 000 bayan an saida ta a kan N10, 500 a kwanakin baya. Akwai kuma wasu kayan da farashinsu bai motsa ba.

Garin Ijebu da farin garin rogo su na nan a yadda aka san su. Haka zalika taliya da jan wake da gas ba su canza ba. Tumaturi da shinkafar Royal Stallion kuwa sun rage kudi ne a makonnin nan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel