Tauraruwa Taylor Swift da Kanye West sun sha gaban duk wani Mawaki a samun kudi
A wannan shekarar, Taylor Swift ba ta da sa’a idan ana maganar samun makudan kudi da waka. Wannan ne karo na biyu da Mawakiyar ta yi zarra a Duniya a cikin shekaru biyar da su ka wuce.
Ga dai jerin nan kamar yadda Mujallar Duniya ta Forbes ta wallafa:
1. Taylor Swift
Fitacciyar Mawakiyar da za ta cika shekaru 30 a Duniya kwanan nan ita ce gaba a sahun samun kudi a bana. A cikin watanni goma sha daya, Taylor Swift ta samu fam Dala miliyan 185 da waka.
2. Kanye West
Kanye West ne ya zo na biyu a jerin. West Mawaki ne kuma Makadi, Mai rubuta waka ya shirya, bayan haka ‘Dan kwalisa ne da ya yi fice a Duniya. A bana kurum ya samu fam Dala miliyan 150.
3. Ed Sheeran
Tauraruwa Ed Sheeran ta na cigaba da haskawa a cikin Matasan Mawaka. Daga farkon bana zuwa yanzu Sheeran ya tara fiye da Dala miliyan 110 kamar yadda Mujallar Forbes ta bayyana.
4. The Eagles
The Eagles Tawagar wasu Mawaka ne da ke Amurka. Sun shafe shekara da shekaru su na waka da ganguna da sarewa da jita. Sun samu kusan Dala miliyan 100 daga wake-wakensu na bana.
KU KARANTA: Wasu 'Yan daudu sun kwan-tsaye su na rafka salloli a Kano
5. Elton John
Elton John wanda shi ma Mawakin Birtaniya ne kamar Sheeran, ya shiga sahun wadanda su ka fi kowa samun kudi da waka a bana. Asusun Elton John ya karu da fam Dala miliyan 84 a 2019.
Ragowar da ke jerin su ne:
6. Shawn Corey Carter ‘Jay-Z’
7. Beyonce Knowles-Carter ‘Beyonce’
8. Aubrey Drake Graham ‘Drake’
9. Sean John Combs ‘P Diddy’
10. Metallica
Jay Z da Mai dakinsa duk sun samu Dala miliyan 81 ne a bana. Drake wanda ya ke biye, ya ci Dala miliyan 75 da waka wannan shekara. Diddy da ya samu Dala miliyan 70 ya na gaban Metallica.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng