Babbar magana: Hotunan yadda aka daura auren wata mata da kafet din dakinta

Babbar magana: Hotunan yadda aka daura auren wata mata da kafet din dakinta

- Bekki mahaifiyar yara biyu ce mai shekaru 26 a duniya

- Saboda tsananin kaunar kafet dinta, ta yanke shawarar aurenshi a matsayin abokin rayuwa

- Bekki ta ce, rayuwarta ba zata zama cikakkiya ba, ba tare da wannan tabarmar ba

Lamarin ya fara ne lokacin da Bekki ta sanar da kawayenta irin tsananin son da take wa kafet dinta. Kawayen nata sun ce basu yi tsammanin maganar aure zata shigo tsakaninta da kafet din ba.

Amma mahaifiyar yara biyun mai shekaru 26 ma'aikaciyar gidan caca, ta bayyana aurenta da kafet dinta a gaban bakin da ta gayyata. Ta hada gagarumin bikin aurensu a inda ta sadaukar da rayuwarta ga kafet din.

Babbar magana: Hotunan yadda aka daura auren wata mata da kafet din dakinta

Babbar magana: Hotunan yadda aka daura auren wata mata da kafet din dakinta
Source: Facebook

Bekki da 'Tabarma' shine sunan da ake kiran ma'auratan. Mahaifiyar yara biyun tana angwanci da mijin nata a gidanta da ke 'Greater Manchester'.

A yayin daurin auren Bekki da kafet dinta, ta yi shiga a cikin kayan gargajiya masu launin fari. Ta yi alkawarin soyayyarshi, karramawa da kula da kafet din har mutuwa ta taba.

Babbar magana: Hotunan yadda aka daura auren wata mata da kafet din dakinta

Babbar magana: Hotunan yadda aka daura auren wata mata da kafet din dakinta
Source: Facebook

KU KARANTA: Tashin hankali: Bidiyon yadda wani dafaffen nama ya koma katon maciji

Bekki ta ce: "Na siyo wannan kafet din shekara daya da ta gabata kuma kowa ya san irin son da nake mishi. Ya fara ne da yadda kawayena ke zolayata 'idan kina son kafet din nan da yawa, me zai hana ki aureshi?'.

"Ina daukar lokaci wajen tsaftaceshi da kaina kuma a kowacce rana. Ina tabbatar da ya fito fes. Ba zan iya kwatanta rayuwa babu shi ba."

Babbar magana: Hotunan yadda aka daura auren wata mata da kafet din dakinta

Babbar magana: Hotunan yadda aka daura auren wata mata da kafet din dakinta
Source: Facebook

Bekki na amfani da abun cire datti idan yaranta biyu sun bata mata 'masoyinta'.

Ubangiji ya basu zaman lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel