Kalaman kaskanci a kan arewa: Gwamna Matawalle ya yi wa Rochas 'wankin babban bargo'

Kalaman kaskanci a kan arewa: Gwamna Matawalle ya yi wa Rochas 'wankin babban bargo'

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya yi kira ga Sanata Rochas Okorocha da ya guji yin kalaman batanci ga arewa, ballantana a yayin da yake tsakar majalisar tarayya.

Matawalle ya kara da bukatar Sanatan da ya fito ya ba mutanen Arewa hakuri a kan "kalaman rashin dacewa da yayi game da matakin karatu a Arewa," wanda ya yawaita a kafafen sada zumuntar zamani.

A wata takarda da mai magana da yawun gwamnan, Zailani Bappa ya fitar, Matawalle ya tabbatar da cewa, akwai yuwuwar Arewa ta zamo koma baya a bangaren ilimi. Amma tozarci ne yadda Sanata Okorocha ya yi maganar.

Matawalle ya kara da cewa, gwamnonin Arewa suna mayar da hankali wajen ganin sun habaka bangaren ilimi.

DUBA WANNAN: Arewa: Jihohi biyar da suka fi talauci a Najeriya da dalilin talaucinsu

Gwamnan ya kara da jan kunnen Okorocha da ya san irin kalaman da zai dinga furtawa, ballantana a kan Arewa da tayi rainonsa.

Kamar yadda takardar ta sanar, gwamnan ya biya kudin jarabawar kammala sakandire sama da naira miliyan 700, kuma zai tura dalibai 200 daga jihar zuwa kasashen ketare don karatun gaba da sakandire.

"Gwamnatin jihar tana gina dakunan karatu 700 na kananan makarantu tare da gyaran a kalla azuzuwa 300 don karin walwala ga malaman jihar. Gwamnan ya ware kashi 19 na kasafin kudin jihar a 2020 don habaka bangaren ilimi," takardar ta kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel