Bai kamata Gwamnati ta raba masarautun kasar Kano ba – Inji Dr. Bashir Aliyu Umar

Bai kamata Gwamnati ta raba masarautun kasar Kano ba – Inji Dr. Bashir Aliyu Umar

A Ranar 7 ga Watan Disamban 2019, Babban Limamin Masallacin nan na Al-Furqan da ke Garin Kano, Bashir Aliyu Umar, ya yi magana a kan raba masarautun jihar Kano a hudunar Juma’a.

Dr. Bashir Aliyu Umar ya ba gwamnatin Mai girma Abdullahi Umar Ganduje shawara a kan kirkirar sababbin Sarakuna. Hakan na zuwa ne bayan kudirin kafa masarautu ya zama doka.

Babban Malamin na Hadisan Manzon Allah da Fiqhun Malikiyyah ya yi tir da yadda doka ta ba gwamna damar zaben wadanda za su rika nada Sarki, ganin irin shaidar da aka yi wa ‘yan siyasa.

A cewar Shehin, masu nada Sarki sun samu wannan daraja ne dalilin Jihadin musulunci da kuma hijira da mubaya’ar da Kakakininsu, su ka yi wa Shehu Danfodio a can shekarun baya.

Limamin ya na ganin ba daidai ba ne siyasa ta nemi ta yi katsalandan a cikin sha’anin Sarakuna. Malamin ya jawo hankalin jama’a a game da yadda gwamnoni su ka rusa kananan hukumomi.

KU KARANTA: Ganduje ya raba kan 'Yan Majalisa da batun kirkirar Masarautu

Malamin ya nuna cewa bai kamata gwamnatin jihar Kano ta Dr. Abdullahi Ganduje ta kawo abin da zai raba kan jama’a tare da jawo sabani ba. Bashir Umar ya nemi gwamnati ta duba maslaha.

Bugu da kari, Limamin ya bayyana cewa Sarakunan da ake da su a kasar Arewa, Sarakuna ne Musulunci ba na gargajiya ba, don haka ya ce bai kamata a taba mutuncin addinin Musulunci ba.

Dr. Umar ya yi kira ga Mai girma gwamnan Kano wanda ake yi wa lakabi da Khadimul Islam, ya cigaba da yi wa addinin Musulunci hidima kamar yadda aka san shi, ya guji ruguza Musulunci.

Wannan huduba da aka gudanar a Masallacin Al-Furqan ta yi daidai da abin da Sheikh Aminu Daurawa ya fada game da barka masarautun Kano, inda ya ce hadin-kai ake nema ba rabuwa ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Online view pixel