Innalillahi: Saurayi ya kashe budurwa ya yanke mata kai ya ciro kwakwalwarta ya dafa ya cinye kamar abinci

Innalillahi: Saurayi ya kashe budurwa ya yanke mata kai ya ciro kwakwalwarta ya dafa ya cinye kamar abinci

- Jami’an tsaro sun cafke wani matashi mai shekaru 21 a kasar Philippines a kan laifin kisan kai

- Bagtong ya hallaka wata mata tare da sassarata gunduwa-gunduwa inda ya cinye kwakwalwarta

- Saurayin ya bayyana yadda ya dafa shinkafa sannan ya kwashi kwakwalwar matar ya ci da ita

An cafke wani mutum da laifin kisan kai a kasar Phillippines bayan da aka zargi ya hallaka wata mata tare da cinye kwakwalwarta.

Lloyd Bagtong matashi ne mai shekaru 21 a duniya, kuma an cafkeshi ne a ranar Alhamis a tsibirin Mindanao bayan da aka ga gawar matar a mil kadan kusa da gidanshi.

An zargi cewa Bagtong ya sanar da ‘yan sanda cewa ya sha barasa ne, kuma yunwa yake ji a lokacin da matar ta yi kokarin mishi magana da safiyar ranar. Ta yi mishi magana da harshen turanci ne, wanda bai ganewa.

“Akwai yuwuwar hakan ya bata wa Bagtong rai,” Kaftin Maribeth Ramoga ya sanar da jaridar Straits Times.

Shaidu sun ce, sun ga Bagtong, wanda bai da aikin yi, yana tafiya tare da matar kusa da inda aka ga gawar matar. Sun zargi cewa, ya kashe matar ne kuma ya yi gunduwa-gunduwa da ita da adda wacce aka gani a sake a kugunshi. Ya yi amfani da wani kyallee wajen daukar kan matar zuwa gidanshi.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Maza masu aure da basa son komawa gida ga matayensu sune suke haddasa cunkoso - Hukumar tsaro

Bagtong ya sanar da ‘yan sandan cewa ya dafa shinkafa ne inda daga nan ya saka kwakwalwar matar a kai ya cinye. Daga nan sai ya wurgar da kokon kan nata a wani rami kusa da gidanshi.

Jami’an ‘yan sandan sun gano gawar matar sanye da wando kadai da kuma hannunta a daure. A halin yanzu, Bagtong na garkame wajen ‘yan sanda kuma an mikashi ga asibitin kwakwalwa don duba lafiyarshi.

Ana cigaba da bincike don gano wacece matar. ‘Yan sanda sun yi kira ga jama’ar da ‘yan uwansu suka bata da su tuntubesu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel