Harkar ilmi: Kudirin Ganduje ya wuce mataki na biyu a Majalisar dokoki
Wani kudiri da zai inganta sha’anin ilmin boko a jihar Kano ya samu karbuwa a majalisar dokoki. Kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto, wannan kudiri ya haura mataki na biyu a zauren.
Kudirin ya fito daga ofishin Mai girma gwamnan jihar Kano ne, inda ya ke neman majalisa ta yi na’am da batun kirkiro wata cibiya ta musamman da za ta bunkasa harkar ilmi a jihar Kano.
A zaman da majalisar ta yi Ranar Talata, ta saurari wannan kudiri a karo na biyu. Wasu daga cikin manyan ‘yan majalisar dokokin jihar sun nuna goyon bayansu game da wannan yunkuri.
Shugaban masu rinjaye a majalisar, Labaran Abdul-Madari, ya nuna cewa idan har kudirin ya samu shiga, kokarin da gwamnatin jihar ta ke yi na wajabta ilmin boko a kyauta zai kai ga ci.
Honarabul Labaran Abdul-Madari ya kuma bayyana cewa majalisar ta Kano za ta yi bakin kokarinta wajen ganin an amince da wannan kudiri da Mai girma gwamna ya aiko da kansa.
‘Dan majalisar ya yi karin haske a game da kudirin, ya na mai cewa idan hakan ta tabbata, cibiyar za ta samu kudinta ne daga cikin asusun IGR na abin da ta ke tatsa da kanta a hannun jama’a.
KU KARANTA: Ganduje ya sa hannu a dokar masarauta bayan amincewar Majalisa
Haka zalika cibiyar za ta rika samun kudi daga hannun sauran kungiyoyin kasashen waje masu bada gudumuwa da kuma gawurtattun Attajiran jihar da kamfanonin da su ke son taimakawa.
Tun ba yau ba, Mai girma gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta shelantawa Duniya cewa ta shigo da tsarin bada ilmin zamani kyauta a matakan firamare da sakandare da ke fadin jihar.
Bugu da kari, zai zama dole kowane yaro ya mallaki ilmin boko a karkashin gwamnatin Ganduje. Za a rika warewa cibiyar kashi 5% na kudin IGR da 2% na kason duka kananun hukumomi.
Idan kudirin ya zama doka a jihar, cibiyar za ta samu shugaba da ma’aikata masu taimakawa da sa-bakin kungiyar PTA. Za kuma a samu wakilai daga kowane yanki a cikin shugabanninta.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng