Risqua Muhammed ya ce N7, 000 rak Janar Murtala ya bari a banki

Risqua Muhammed ya ce N7, 000 rak Janar Murtala ya bari a banki

Risqua Muhammed, ‘Dan tsohon shugaban Najeriya, Janar Murtala Ramat Mohammed, ya bayyana adadin kudin da Mahaifinsa ya bari a asusun bankinsa a lokacin da ya bar Duniya.

Alhaji Risqua Muhammed ya ce Marigayi Murtala Ramat Mohammed, ya bar N7000 ne rak a cikin akawun dinsa na banki duk da cewa shi ne shugaban kasa a lokacin da ya mutu a farkon 1976.

A Ranar Litinin, 2 ga Watan Disamban 2019, Risqua Muhammed ya yi wannan bayani a lokacin da ya ke jawabi wajen kaddamar da wani mutum-mutumi da aka gina domin tunawa da Marigayin.

Kamar yadda mu ka ji, an gina mutum-mutumin Janar Murtala Mohammed ne a wajen shiga cikin dakin taron manyan Daliban jami’ar Obafemi Awolowo da ke Garin Ile-Ife a cikin jihar Osun.

KU KARANTA: Yadda aka kashe Janar Murtala Mohammed ya na hanyar ofis

Muhammed ya ce Mahaifinsa ya yaki rashin gaskiya da satar dukiyar al’umma a lokacin da ya ke mulki a matsayin shugaban kasa. Tsohon shugaban kasar ya mutu ne shekaru 43 da su ka wuce.

A cewar Muhammed, Janar Ramat, ya mulki Najeriya da gaskiya a tsawon kwanaki 200 da ya yi a ofis. Haka zalika ya yi kira ga mutanen kasar nan su mara baya ga yakin da Buhari ya ke yi.

Shugaba Muhammadu Buhari mai ikirarin yakar rashin gaskiya ya fara rike babban mukami ne a lokacin mulkin Janar Murtala Mohammed. A wancan lokaci ne Buhari ya zama gwamnan jiha.

A na sa jawabin, shugaban jami’ar OAU, Farfesa Eyitope Ogunbodede, ya yaba da yadda ‘Daliban jami’ar su ka tuna da tsohon shugaban da aka kashe ba tare da ya mutu ya bar kudin sata ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel