Hukumar EFCC ta gano Makarantar koyon zamba da damfara a Akwa Ibom

Hukumar EFCC ta gano Makarantar koyon zamba da damfara a Akwa Ibom

Jami’an hukumar nan ta EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa a Najeriya, sun gano wani mugun wuri da ake zargin ana koyawa jama’a dabarun damfara.

Kamar yadda rahotanni su ka zo mana, Dakarun hukumar ta EFCC sun yi nasarar bankado wannan wuri ne a wani Kauye da ake kira Ikot Ibiok da ke karamar hukumar Eket a Akwa-Ibom.

Wannan gida da aka ajiye mutanen da ake horaswa domin su zama rikakkun masu damfara da zamba ya na nan a kan layin Esien da ke wannan Kauye na Ikot Ibiok a yankin Kudancin kasar.

Babban jami’in yada labarai na hukumar EFCC, Wilson Uwajaren, shi ne ya bada wannan sanarwa. Uwajaren ya ce sun kama mutane 23 da ake zargin cewa masu laifi ne a wannan hari.

KU KARANTA: Yahoo-Yahoo: Hukumar EFCC ta ci kasuwa a Jihar Enugu

Dakarun hukumar sun kai wannan samame ne a safiyar Ranar Alhamis 28 ga Watan Nuwamban 2019. Wadanda aka kama Matasa ne masu shekara 19 zuwa 35 kamar yadda EFCC ta bayyana.

Wadanda aka cafke sun tabbatarwa hukumar cewa ana koya masu yadda ake tafka ta’adi iri-iri ta yanar gizo da makamantansu. Daga cikin irin abubuwan da ake koya masu dai har da damfara.

Bugu da kari ana nunawa wadannan Matasa yadda za su samu kudi a yanar gizo da soyayyar bogi, da cinikin karya da ma fakewa da sunan wani domin a yaudari mutane ta kafefen zamani.

EFCC ta tabbatar da cewa wadanda aka kama sun fadi yadda aka shigo da su cikin harkar. A cewar wadanda ake zargin, an daurawa kowa nauyin ayyukan da zai rika yi a makarantar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel