Tinubu da Saraki zasu kafa jam'iyyar da zata karya APC kafin 2023 - Owolabi

Tinubu da Saraki zasu kafa jam'iyyar da zata karya APC kafin 2023 - Owolabi

- Tun kafin a fita daga shekarar da aka sake zaben shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a karo na biyu, masu son takara a 2023 sun fara kulle - kulle

- Wani babban malamin addinin Kirista a jihar Kwara ya ce jam'iyyar APC zata tarwatse kafin shekarar 2023

- Ya yi hasashen cewa wata sabuwar jam'iyya da Tinubu da Saraki zasu kafa, zata kawo karshen mulkin APC a zabe na gaba

A yayin da manyan 'ya'yan jam'iyyar APC ke kulle-kullen ganin yadda zasu gaji kujerar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, bayan ya kammala zangon wa'adinsa na biyu a shekarar 2023, wani malamin addinin Kirista mai ikirarin ganin gobe ya ce APC zata tarwatse.

A cewar Christpher Owolabi, babban malami a Majami'ar CAC (Christ Apostolic Church) da ke yankin Ori–Oke a Irapada, jihar Kwara, "APC ba zata iya cimma burinta na kafa gwamnati a shekarar 2023 ba".

Owolabi ya bayyana takaicinsa bisa salon mulkin jam'iyyar APC tare da yin fatan cewa Allah ba zai bar jam'iyyar APC ta rayu zuwa shekarar 2023 ba.

DUBA WANNAN: Sahihan dalilan da suka sa aka tunbke kakakin majalisar jihar Taraba

Da yake gana wa da manema labarai a Omu - Aran, Owolabi ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, da takwaransa na jihar Kwara, Bukola Saraki, zasu kafa jam'iyyar da zata maye gurbin APC a 2023.

Ya kara da cewa wasu manyan mutane hudu, masu 'fada a ji' da taka muhimmiyar rawa wajen samun mulki a Najeriya, zasu mutu kafin shekarar 2023 tare da bayyana cewa akwai bukatar jama'a su dage da yi wa kasa addu'o'i.

Owolabi ya jaddada cewa yana da yakinin shugaba Buhari zai gurgunta jam'iyyar APC kafin ya bar Ofis, lamarin da ya bayyana cewa zai bawa sabuwar jam'iyyar da su Tinubu zasu kafa damar cin zabe tare da kawo wa Najeriya cigaba a cikin shekaru hudu na farko da zata yi a kan karagar mulki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel