Tarihin rayuwa da siyasar Sanatan Kogi ta Yamma Smart Adeyami

Tarihin rayuwa da siyasar Sanatan Kogi ta Yamma Smart Adeyami

1. Haihuwa

An haifi Smart Adeyami ne daf da Najeriya za ta samu ‘yancin kai daga Turawan mulkin mallaka, a Ranar 18 ga Agustan 1960. Wannan na nufin Sanatan ya na da shekaru 59 yanzu a Duniya.

2. Karatu da aiki

Smart Adeyami ya yi karatu a Garinsu har ya zarce ya zuwa Makarantun gaba da Sakandare. Adeyami ya samu shaidar PGD a bangaren hulda da jama’a. Sannan kuma ya na da Difloma a fannin shari’a da wata babbar diflomar a sha’anin yada labarai wanda ya sa ya zama ‘Dan jarida.

Shafinsa na Wikipedia ya nuna Adeyamu ya yi karatun Digirgir watau Masters a bangaren hulda da jama’a da ya samu shaidar PGD. Ya yi wannan karatu ne a jami’ar fasahar tarayya ta Owerri.

A bangaren aiki, Smart Adeyami ‘dan jarida ne kuma har ya rike shugaban kungiyar nan ta ‘yan jaridan Najeriya na kasa baki daya. Adeyami ya rike wannan mukami tun daga 1999 hae 2006.

3. Siyasa

2007

Bayan sauka daga kujerar NUJ, Adeyami ya nemi takarar Sanata a mazabarsa ta Yammacin Kogi. An yi dace ya yi nasarar zama ‘dan majalisar dattawa, ya gaji Jonathan Tunde Ogbeha a 2007.

KU KARANTA: 'Yan siyasan Kogi da su ka takawa Dino Melaye burki

2011

A shekarar 2011, Adeyami ya sake takarar ‘Dan majalisa a jam’iyyarsa ta PDP, ya kuma lashe zabe. Sai dai daga baya kotu ta rusa zaben fitar da gwanin da jam’iyyar PDP ta shirya a lokacin.

Sanata Adeyami ya sake samun kyakkyawar galaba a kan babban abokin hamayyarsa Abiye Abinso. Wannan ya sa koma kujerarsa. Ya kuma rike mukamai a kwamitoci da dama a majalisar.

2015

Smart Adeyami bai samu sa’ar komawa majalisa a zaben 2015 ba, ya sha kashi ne a hannun Dino Melaye na jam’iyyar APC. Daga baya kuma ‘yan siyasan su ka yi hannun riga da jam’iyyunsu.

2019

Bayan komawar Dino Melaye PDP, sai Smart Adeyami ya sheka APC. Dino ya sake lashe zaben 2019. Jim kadan kotu su ka rusa wannan zabe na farkon 2019, su ka umarci a sake sabon zabe.

Smart Adeyemi ne ya lashe zaben da aka sake yi a Nuwamban 2019, daga farko an gaza kammala zaben, amma a karshe INEC ta tabbatar jam'iyyar APC ta yi nasara da ratar kuri’a fiye da 26, 200.

Wannan na nufin Sanatan da ya saba mikewa a zaure zai koma majalisar tarayya a karo na uku.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel