Kyawawan Hotuna: Wasu ma'aurata Hausawa da suka yi auren soshiyal midiya sun bayyana labarin soyayyar su mai ban mamaki

Kyawawan Hotuna: Wasu ma'aurata Hausawa da suka yi auren soshiyal midiya sun bayyana labarin soyayyar su mai ban mamaki

- Komai da zaka gani ya faru, akwai tushenshi ko mafarin shi, ballantana aure ko soyayya

- Wasu masoyan kan hadu a makaranta, titi, biki, asibiti ko kuma dai a kasuwa

- Ga wasu masoyan da suka ci ribar soyayya ta hanyar aure, sun bada bayanin yadda suka hadu da juna

Bahaushe dai na cewa soyayya gamon jini. Ba a haduwa da saurayi yau a aureshi gobe. Ko kuma zamu iya cewa, kowanne masoya da ka gani, toh tabbas akwai wani labari mai dadi ko akasin hakan da ya zamo tushen soyayyar tasu.

Wasu tarin ma’aurata sun bayyana yadda suka hadu da juna a kafafen sada zumuntar zamani tare da labarin soyayyarsu.

Wata mai suna Ummieta Rabiu, ta yi bayanin yadda suka hadu da nata mijin kuma rabin rayuwarta. Ta hadu dashi ne a kafar sada zumuntar zamani ta tuwita. Tana da shekaru 17 inda yake da 23. Sun yi soyayyar shekaru bakwai inda daga baya suka angwance. A halin yanzu dai shekarunsu hudu da aure cikin zaman lafiya da kaunar juna.

KU KARANTA: To fah: A shirye nake na auri kamaye a zahiri idan har zai yarda - Adama jarumar Dadin Kowa

“Mun hadu ne a tuwita, ina da shekaru 17 shi kuma yana da 24. Mun yi soyayyar shekaru 7 inda daga baya muka yi aure. A halin yanzu muna da shekaru 4 da aure.” In ji Ummeeta.

Hotuna: Wasu ma'aurata Hausawa da suka yi auren soshiyal midiya sun bayyana labarin soyayyar su mai ban mamaki
Hotuna: Wasu ma'aurata Hausawa da suka yi auren soshiyal midiya
Asali: Facebook

Ita kuwa Khadija ta ce: “Mun hadu a tuwita a shekaru 8 da suka gabata. Ina da shekaru 20. Mun yi shekaru hudu da aure, amma babu abinda zan ce sai godiya ga Allah domin kuwa ya albarkace mu da ‘ya mace.”

Hotuna: Wasu ma'aurata Hausawa da suka yi auren soshiyal midiya sun bayyana labarin soyayyar su mai ban mamaki
Hotuna: Wasu ma'aurata Hausawa da suka yi auren soshiyal midiya
Asali: Facebook

Malam Anas kuwa yayi bayanin cewa, ya hadu da matarshi uwar ‘ya’yan shi biyu a kafar sada zumuntar zamani ta Facebook ne. Tana da shekaru 21 inda shi yake da 25. Sun yi aure a 2012. A halin yanzu shekarunsu bakwai da aure. Allah ya albarkacesu da ‘ya’ya biyu.

Hotuna: Wasu ma'aurata Hausawa da suka yi auren soshiyal midiya sun bayyana labarin soyayyar su mai ban mamaki
Hotuna: Wasu ma'aurata Hausawa da suka yi auren soshiyal midiya
Asali: Facebook

Wata kuwa mai suna Cicaeda kamar yadda ya nuna a shafinta na tuwita, ta ce “Mun hadu dashi ne tun muna makarantar sakandire. Ina da shekaru 13 inda yake da 16. Shekaru 16 kenan da suka gabata. Mun yi aure tun shekaru 7 da suka gabata. Hukunci mafi muhimmanci da muka yanke.”

Hotuna: Wasu ma'aurata Hausawa da suka yi auren soshiyal midiya sun bayyana labarin soyayyar su mai ban mamaki
Hotuna: Wasu ma'aurata Hausawa da suka yi auren soshiyal midiya
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel