Jam'iyyar APC ta naɗa wani na kusa da Jonathan muƙami a Bayelsa

Jam'iyyar APC ta naɗa wani na kusa da Jonathan muƙami a Bayelsa

- Rade-radin cewa Dr Goodluck Jonathan na da ra’ayi a sabuwar gwamnatin jihar Bayelsa ya tabbata

- Tsoffin shuwagabannin Najeriya ma’abota biyayya ne aka nada a cikin kwamitin karbar sabuwar gwamnatin

- Kwamitin ya kunshi mutane 59 wanda tsohon mataimakin gwamnan jihar, Rt Hon Wrinipre Seibarugu ke jagoranta

Sabon zababben gwamnan jihar Bayelsa, David Lyon, ya nada makusancin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan cikin kwamitin karabar mulkin jihar da APC zata yi a watan Fabrairu na 2020.

Kwamitin mutane 59 ya samu shugabancin tsohon gwamnan jihar, Rt Hon Werinipe Seibarugu.

Gwamna Seriake Dickson ya nada kwamitin mika mulki, wanda ya samu shuagabancin sakataren gwamnatin jihar, Kemela Okara kuma ya kunshi duk kwamishinonin jihar na yanzu.

DUBA WANNAN: EFCC ta cafke 'Ibrahim Magu' na bogi kan zargin karbar rashawa

Jaridar Daily Sun ta ruwaito cewa, kwamitin mutane 59 ya kunshi har da tsohon shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar, Chief Obegha Julius Oworibo a matsayin sakatare.

Kwamitin ya kunshi tsoffin ‘yan takarar gwamna, makusantan Jonathan, dattijan jam’iyya, shuwagabannin jam’iyya da ‘yan majalisar tarayya.

Wasu daga cikin sanannun mutanen da ke cikin jerin sunayen sun hada da tsoffin ‘yan takarar gwamnan jihar, Yarima Ebitimi Angbare, Farfesa Ongoebi Maureen Etebu da CP Dieseye Poweigha.

Sanannun makusantan Jonathan kuwa sun hada da Rt Hon Claudius Enegesi Injiniya Mike Ogiasa da Chief Moses Otazi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164