Rabiu Kwankwaso ya ziyarci Bala Mohammed a gidan Gwamnatin Jihar Bauchi

Rabiu Kwankwaso ya ziyarci Bala Mohammed a gidan Gwamnatin Jihar Bauchi

Jagoran Kwankwasiyya a Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya tashi ta-ka-nas ta Kano, ya kai ziyara wajen gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulqadir Mohammed.

Kamar yadda mu ka samu labari dazu, ‘yan siyasar sun yi wannan ganawa ne a gidan gwamnati a jiya Ranar Laraba, 27 ga Watan Nuwamban 2019 a cikin Garin Bauchi da ke jihar.

Manyan ‘yan siyasar adawar kasar sun yi ganawarsu ne a bayan labule ba tare da ‘yan jarida sun san abin da su ka tattauna ba. Bayan kus-kus din, sun zanta da Manema labarai.

A cewar tsohon gwamnan na Kano, Injiniya Rabiu Kwankwaso, ya kawowa Mai girma gwamnan Bauchi da ya kira Aboki kuma ‘Danuwansa wannan ziyara ne domin taya sa murna.

Sanata Musa Kwankwaso ya ce tun da Sanata Bala Mohammed ya dare kan kujerar gwamna, bai samu damar zuwa domin ya yi masa murnar lashe zaben na 2019 da aka yi ba.

KU KARANTA: 'Yan siyasan da PDP za ta tsaida idan ta na so ta doke APC a 2023

Idan ba ku manta jihar Bauchi ta na cikin inda PDP ta karbe mulki a zaben bana. Bala Mohammed ya tika gwamna mai-ci na jam’iyyar APC watau Mohammed Abubakar da kasa.

Hadimin tsohon Sanatan na Kano ne ya wallafa wannan hotuna da bidiyoyi inda ya rubuta: “@KwankwasoRM tare Da zababben Gwamnan Jihar Bauchi @SenBalaMohammed...

...Saifullahi Hassan wanda ya ke daukan babban ‘dan siyasar hoto ya kara da cewa: “Bala Muhammad (Kauran Bauchi), a yau (jiya yanzu) Laraba A Fadar Gwamnatin Jihar Bauchi."

A wani bidiyo na dabam an hangi Mai girma gwamnan da kansa ya na budewa tsohon Ministan tsaron kasar kofar mota, inda shi kuma ya shiga, ya yi masa godiyar wannan ziyara.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel