Rahama Sadau: Dalilin da yasa bana mayar da martani ga masu zagi

Rahama Sadau: Dalilin da yasa bana mayar da martani ga masu zagi

- Fitacciyar jaruma Rahama Sadau ta bayyana burinta a rayuwa, tare da dalilin da yasa bata mayar wa mutane martani a kan batanci

- Jarumar ta ce, burinta bai wuce ta yi fim din da zai taba rayuwar mutane sannan ya mika sakonni ga mutanen kasar Hausa ba

- Rashin mayar da batanci da jama’a ke mata kuwa, ya biyo bayan tsarin rayuwar wacce ta ke koyi da ita ne, Priyanka Chopra

Fitacciyar jarumar fina-finan hausa, Rahama Sadau, ta bayyana cewa tana da burin da ta dade tana dakon shi, domin ta shirya fim din da zai ilimantar da al’umma tare da taba rayuwa da matsalolin da ake fama dasu a kasar Hausa.

Ta kara da cewa, wannan dalilin yasa ta shirya fim karkashin kamfaninta na Rariya domin nunawa duniya yadda rayuwar yara ‘yan mata ta ke tafiya a yanzu. Sannan iyaye da basu saka ido a kan ‘ya’yansu, su ga yadda rayuwar yara mata ta ke lalalcewa a wannan zamani.

Bayan haka, jarumar ta kara yin kira da babbar murya ga iyayen yara, da su ke tura yaransu jami’o’I ba tare da sun san inda suke sauka ba, kuma su tsaya su yi bincike da irin mutanen da yaran su ke tarayya dasu a makaranta. Saboda zama da marasa tarbiyya na saurin canzawa yara hali.

Ta kuma yi Allah wadai da manyan mutane da ke boye a gefe guda, wadanda basu da wani aikin da ya wuce lalata da kananan yara ‘yan makaranta, ta hanyar basu manyan kudi saboda su kashe zuciyarsu har su saba musu da irin wannan mummunan hali.

KU KARANTA: Masu abu da abun su: Zahra Buhari za ta hada wani gagarumin taro da zai jawo hankula a wannan makon

Jarumar ta bayyana jin dadinta saboda sakon nata ya isa inda take so ya kai. Domin a cewarta mutane da dama a fadin kasar nan, harda na kasashen ketare sun kalla sun kuma yaba da irin namijin kokarin da ta yi wajen isar da wannan sakon.

Sai dai kuma, duk da wannan kokarin da jaruma Rahama Sadau ta yi, ta koka cewa wannan bai hanata daukar zagi daga wajen mutane ba duk lokacin da ta yi abu, komai kankantarshi.

Rahama Sadau na daya daga cikin matan masana’antar Kannywood da ta ta fi kowa fuskantar kalubale, saboda irin shigar da ta ke yawan yi a duk lokacin da za a yi karo da ita a fili ko a shafukan soshiyal midiya.

Da aka tambayeta dalilin da yasa bata mayar da martani a kan duk caccakarta da akeyi, sai tace: Ita tana koyi ne da jaruma Priyanka Chopra ta kasar Indiya. Jarumar kuwa bata mayar da martani ga duk abinda za a ce a kanta. Wannan dalilin ne yasa bata tankawa zagi ko batanci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel