Daya daga cikin masu kudin Singapore, Yung Chung ya na zuwa ofis a shekara 101

Daya daga cikin masu kudin Singapore, Yung Chung ya na zuwa ofis a shekara 101

Mun samu labari cewa a shekara 100 – da ‘yan kai a Duniya, har gobe Chang Yung Chung ya na zuwa aiki a ofis. Wannan mutumi mai shekaru barkatai ya ba Dala biliyan 1.6 baya a yanzu.

Idan ana kawo jerin masu dukiya a Duniya, Chang Yung Chung, shi ne wanda ya fi kowa tsufa a cikin wannan sahu na kasurguman Attajirai. Ya na da shekara 101, kuma ya na nan garau.

Abin da ke cikin asusun wannan Dattijo shi ne biliyan $1.6. Idan aka lissafa wannan kudi a Naira ya kai N578, 400, 000, 000. Mujallar Forbes ta ce wannan bai hana Yung Chung zuwa ofis ba.

Mista Yung Chung ya yi arziki ne da jigilar kaya watau fatauci ta jiragen ruwa. A shekarar bara ta 2018, Attajirin ya damka kamfanin jirgin ruwansa na Pacific International Lines ga wani ‘Dansa.

Teo Siong Seng shi ne ya gaji Mahaifin na sa a 2018, yayin da wannan tsoho ya koma rike da mukamin babban shugaba na wannan kamfani domin kula da harkokin da ake yi na yau da gobe.

KU KARANTA: NBS ta wallafa rahoto mai dadi game da tattalin arzikin Najeriya

Ana tunanin cewa Yung Chung ya ki rabuwa da kamfanin har yanzu ne saboda irin asarar da Pacific International Lines ta tafka a bara, wannan kamfanin jirage ya rasa kudi har miliyan $200.

Lissafin kudin Najeriya ya nuna cewa abin da kamfanin ya rasa a bara ya haura Naira biliyan 75. Bugu da kari, ta-ta-burzar da ake yi tsakanin Amurka da kasar Sin ya na dada taba kamfanin.

Tun 1967 wannan kamfani ya fara aiki a Duniya, Chung Chung ya jagoranci Pacific Lines na tsawon shekaru fiye da 50 har ya kai inda ya kai kafin ya mika ragamarsa ga yaron da ya haifa.

Siong Seng ya na sa rai abubuwa za su gyaru nan gaba bayan ya shekara guda a ofis. Kamfanin zai rika amfani da wata fasahar zamani domin iya gane duk inda jiragensa su ke a cikin ruwa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel