Dakarun NAF sun kashe shugabanin ISWAP yayin da suka tarwatsa wurin taron su

Dakarun NAF sun kashe shugabanin ISWAP yayin da suka tarwatsa wurin taron su

Rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF) ta kashe wasu shugabanin kungiyar Islamic State of West Africa Province, ISWAP, tare da lalata wurin taron su a Jubillaram a arewacin jihar Borno.

Mai magana da yawun NAF, Ibikunle Daramola ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba a Abuja.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa ya ce Maharan sama, ATF na Operation Lafiya Dole suka kai harin ne a ranar Talata.

Ya ce, "An kai harin ne a jiya 19 ga watan Nuwamba bayan samun bayannan sirri dake nuna cewa wasu manyan shugabannin ISWAP sun hadu don yin taro a wani gida a yankin da suke amfani wurin ajiye wasu kayayyakin zirga-zirga.

DUBA WANNAN: Abinda Buhari ya fadi min a kan Yari - Sanata Yarima

"Hakan yasa ATF ta aike da jiragen leken asiri da na yaki domin su kai hari a wurin.

"An hango wasu 'yan ta'adda da dama kusa da wasu gine-gine a cikin gidan da ke tsakiyar garin.

"An yi musu luguden wuta ba kakautawa a yayin da suka yi yunkurin tserewa.

"An yi nasarar lalata gidajen 'yan ta'addan ciki har da dakin da suke ajiyar muhimman kayayyakinsu da aka hango ya kama da wuta."

Daramola ya ce NAF za ta cigaba da hadin gwiwa da sauran sojojin kasa domin ganin an kawo karshen 'yan ta'addan da suka yi saura a yankin na Arewa maso gabas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel