'Yan bindiga sun sace mai jego da wasu mutane 5 a cikin garin Kaduna

'Yan bindiga sun sace mai jego da wasu mutane 5 a cikin garin Kaduna

Wasu 'yan bindiga sun kai hari tare da yin awon gaba da wata mata 'mai jego' da sauran wasu mutane biyar a unguwar Dan Mani da ke yankin karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Lamarin, wanda shine na farko a unguwar, ya faru ne da misalin karfe 3:15 na safiyar ranar Laraba.

Mazauna yankin da abin ya faru sun bayyana cewa 'yan bindigar sun yi ta harbe-harbe bayan isarsu unguwar, mai makwabtaka da Falwaya, lamarin da suka ce ya hana su cigaba da barci saboda fargaba.

Daya daga cikin mai unguwannin yankin da abin ya afku ya tabbatar wa da jaridar Daily Trust faruwar lamarin tare da bayyana cewa mazauna unguwar da kewaye sun matukar firgita da sace mutanen da 'yan bindigar suka yi.

"Tabbas mun shiga rudani sakamakon sace mutane 6 da 'yan bindiga suka yi, a cikin mutanen da suka sace akwai maza hudu, mata biyu; kuma acikinsu har da wata mai jego da takecauren wani mutum mai suna Gali. Sun tafi da ita saboda mijinta ya samu ya kubuta.

"Daga cikin ragowar mutanen da aka sace akwai wani mai suna Gambo da Bukar Mandara da sauransu. Dukkan mutanen 6 da aka sace talakawa ne," a cewarsa.

Ya kara da cewa 'yan bindigar sun kira matar daya daga cikin mutanen da suka sace tare da sanar da cewa suna bukatar kudin fansa da yawansu ya kai miliyan N10.

Mai unguwar ya yi kira ga gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, da ya kawo musu agaji ta fuskar tsaro saboda kalubalen tsaro da suke fuskanta a yankinsu.

Da jaridar Daily Trust ta tuntubi kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo, ya ce yana cikin wani taro amma zai kira su daga baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel